WASIKU
KU DAINA WULAKANCI
Daga Maryam Y.
Ballah
+234 806 066 6637
INA so edita ya ba ni dama in mik'a sak'on gaisuwa ga duk masu
buga min waya ko sak'o ta hanyar I-mel. Allah ya saka ma su da alheri.
Sannan ina son in tambayi matan fim dalilin da ya sa ba su son amsa
waya idan mutum ya buga ma su, ko ta hanyar turo ma su sak'o? Gaskiya
ku daina wulak'anci. Saboda in ku ne yau gobe ba ku ba ne. Abin
da ya sa na fa]i haka shi ne a kullum in ana hira da ku sai ku ce
ai duk wanda ya ce ya na son ka ya gama maka komai. Amma a zuciyar
ku ba haka abin ya ke ba. Ina yi wa Maryam A. Baba godiya saboda
na buga mata waya ta kuma amsa min. Gaisuwa mai tarin yawa ga Zainab
Idris, Zainab Indomi, Sadiya Gyale, Sani Musa Danja, Ibrahim Maishunku,
Yusuf Ubale, da Ali Nuhu. Fatan alheri ga Binta I.S.I. dangane da
auren da ta yi. Allah Ya ba da zaman lafiya da alherin da ke cikin
aure.
AI GA IRIN TA NAN!
Daga Muhammad
Adamu Salihu
Giginyu Qrts, Nassarawa, Kano
+234 805 625 4042,
+234 703 608 7606
ZAN yi matuk'ar farin ciki idan edita zai ba ni gurbi a cikin wannan
mujalla mai albarka da farin jini domin in yi kira da ba da shawara
ga ’yan fim a kan wani abu da na karanta a Fim ta watan da
ya gabata, wanda zama a cikin irin wannan yanayi ga wasu tsirarun
’yan fim zai iya kawo ~araka da koma baya a cikin harkar gaba
]ayan ta. Abin kunya ne a ce ana samun irin haka a cikin wa]anda
su ke kiran kan su da sunan masu fa]akarwa. Ya kamata dai ’yan
fim a yi karatun ta-natsu. Tunda masu iya magana sun ce idan ka
ga gemun ]anuwan ka ya kama da wuta, to sai ka shafa wa na ka ruwa.
Kuma an ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.
Duk fa wannan batu da na ke yi ba wani abu ba ne face shiri da
zaman lafiya da kuma daidaito a tsakanin ’yan fim. Duk wanda
ya karanta Fim ta watan jiya na tabbatar ya ci karo da inda aka
yi hira da ’ya’yan marigayiya Hajiya Jamila Haruna,
inda ]aya daga cikin su ta ke cewa ita marigayiyar ta na fa]a mata
cewa Ali Nuhu ne kawai ba su shiri da shi daga cikin abokan sana’ar
su. Mai yiwuwa Allah Ya so ta da rahama ne Ya sa ta farga har ta
kira shi a waya. Shi ma kan sa Alin ya tabbatar da hakan, inda a
cikin mujallar ya ce ’yan kwanaki kafin rasuwar ta ta yi masa
sak'o ta wayar GSM. Na tabbatar da ya san za ta rasu a cikin wa]annan
‘ya’ kwanakin da ya yi k'ok'arin ba ta amsa, ko ma ya
kira ta su shirya. To ’yan fim, ya kamata dai a ha]a kai a
ba mara]a kunya. A daina samun rabuwar kai a tsakani. Ana gani dai
yau a ce wane ya mutu gobe a ce su wane sun mutu, kuma duk a ha]arin
mota. Da fatan Allah Ya jik'an duk wa]anda su ka mutu, Ya yi masu
rahama. Mu kuma idan tamu ta zo Allah Ya sa mu cika da imani. Gaisuwa
ta musamman da ta’aziyya ga Alhaji Ibrahim Sheme bisa rasuwar
da Allah Ya yi wa mai]akin sa a Kano. Da fatan Allah Ya kai rahama
ga makwancin ta, Ya kuma albarkaci abin da ta bari. Ga ’yan
fim kuma, idan kunne ya ji, jiki ya tsira.
MU TAYA SANI ADDU’A
Daga Ibrahim 2-Effect
No.13 Dutse Road, Kakuri, Kaduna
+234 805 928 4228,
+234 703 456 5243,
GASKIYA mun yi matuk'ar bak'in cikin abin da ya faru ga Sani Musa
Danja. Wallahi ba mu ji da]i ba ko ka]an. Allah Ya k'ara kare gaba.
Wa]anda su ka yi k'ok'arin ]auke mashi ku]a]e da kayayyakin shi
kuma, su sani Allah na sane da su. Da fatan za mu ci gaba da taya
shi addu’a Allah Ya ba shi sauk'i. Gaisuwa ga Sani Danja,
Yakubu Muhammed, Ubale Wanke-wanke, T.Y. Shaba, Sani Maikatanga,
Aliyu Gora II, da Samira Ahmed.
ABIN A YABA NE
Daga Usman Adamu
Aliero,
Jihar Kebbi, Nijeriya
+234 808 205 7030
DA farko ina taya wannan mujalla mai farin jini murnar cika shekara
10 da kafuwa. Hak'ik'a wannan abin a yaba ne ga mu mutanen arewacin
k'asar nan da ma Nijeriya gaba ]aya dangane da yadda ta ke fitowa
ba tare da fashi ko da sau ]aya ba. Wannan ya nuna irin tsarin ma’aikatan
ta masu k'ok'arin bunk'asa harshen Hausa. Allah Ya k'ara ba ku k'arfin
gwiwar ci gaba da wannan k'ok'ari. Ina yi wa iyalan marigayiya Jamila
Haruna ta’aziyyar rasuwar ta. Allah Ya jik'an ta da rahamar
sa. Ina yi wa Sani Danja jajen ha]arin da ya samu. Shi ma Allah
Ya ba shi lafiya. Saura kuma Allah Ya kare ku daga fa]awa muguwar
hanya. Ina taya wa]anda su ka yi aure murna. Wa]anda ba su yi ba
Allah Ya ba su nasu mazajen, kamar su Jamila Nagudu da sauran su.
Daga k'arshe ina gaida Sani Danja, Ali Nuhu, Adam A. Zango, Jamila
Nagudu da Alubanku]i.
ALLAH YA GAFARTA MA TA
Daga Muhammed
Jungudo,
Yola, Jihar Adamawa
+234 703 492 4275
INA mik'a sak'on ta’aziyata ga Ibrahim Sheme dangane da rasuwar
matar sa Binta. Allah Ya gafarta mata, Ya sa ta huta, amin.
ALLAH YA JIKAN JAMILA
Daga Muhammad
Yahaya Gumel (Danhajiya)
No. R3, opp. Abeokuta Street, Mando, Kaduna,
+2348039730648
INA yi wa dukkan ma’aikata tare da makaranta wannan mujalla
mai tarin albarka a duk inda su ke fatan alheri. Bayan haka, ina
so in yi amfani da wannan dama in mik'a sak'on ta’aziyya ga
dukkan ’yan’uwa da abokan arzik'i da masu wannan sana’a
ta fim ta’aziyyar rashin da mu ka yi na Jamila Haruna da matar
Ibrahim Sheme. Da fatan Allah Ya jik'an su, Ya kuma sa sun huta.
Ta ~angare guda kuma ina yi wa Sani Musa Danja addu’ar Allah
Ya ba shi lafiya game da ha]arin da ya rutsa da shi. Ina kuma taya
dukkan wa]anda su ka samu k'aruwa ta yin aure murna. Da fatan Allah
Ya albarkaci auren nasu, Ya kuma ba su zaman hak'uri da lafiya.
Wa]anda su ka rage kuma su ma Allah Ya nuna mana nasu.
ALLAH YA JIKAN BINTA
Daga Hon. Abdullahi
Ubandawaki,
Gudu L.G.A, Jihar Sokoto,
0806685530
YAN’UWA ’yan kulob ina yi maku sallama irin ta addinin
Islama kamar kullum. Bayan haka, ina mik'a sak'on ta’aziyya
ta ga Ibrahim Sheme a kan rasuwar matar sa. Ubangiji Ya jik'an ta
da rahama, Ya kuma sa Aljanna Firdausi ce makomar ta. Mu kuma idan
ta mu ta zo Allah Ya sa mu cika da imani.
SAKON TA’AZIYYA DA JAJE
Daga Rabi’u
Yunusa,
Abbatuwa, Agege, Legas,
+234 802 944 3333
INA mik'a sak'on ta’aziyya ta ga ’yan’uwa da
abokan sana’ar marigayiya Jamila Haruna. Allah Ya jik'an ta,
ya kuma gafarta ma ta amin. Ina kuma taya Tahir I. Tahir, Binta
I.S.I. da Auwal West murnar auren da su ka yi. Allah Ya ba su zaman
lafiya da ’ya’ya nagari. Sak'on jaje ga Sani Danja dangane
da ha]arin mota da ya rutsa da shi. Allah Ya ba shi lafiya. Gaisuwa
ga abokn arzik'i na irin su Musa, Nasiru Kwatakwalli, Adam B. Adam,
Inuwa Niga, Maman Bilal Festak, da dukkan makaranta mujallar Fim
na garin Legas.
TA’AZIYYA GA SHEME
Daga Bello BG,
Gidanmadi, Sokoto,
+2348060037979, +2348022186767
NA yi matuk'ar farin cikin samun damar isar da sak'on ta’aziyya
ga Ibrahim Sheme da ]aukacin ma’aikatan mujallar Fim dangane
da rasuwar Malama Binta, matar Ibrahim Sheme. Allah Ya gafarta mata
dukkan kurakuran ta, Ya kuma sa Aljanna ce makomar ta. Mu kuma Allah
Ya sa mu cika da imani.
KI CANZA RAYUWAR KI
Daga A’isha
Abuja, +2348058061357
INA so edita ya ba ni dama a cikin wannan mujalla mai albarka da
]aukaka in yi kira da nasiha ga ’yar wasa Maryam Indiya. A
gaskiya irin halin da na gan ki ciki a Legas
ban ji da]i ba. Don haka ina ba ki shawara da ki canza rayuwar
ki. Gaisuwa ga dukkan ma’aikatan mujallar Fim.
ALLAH YA GAFARTA MA TA
Daga Hajiya Ramatu,
Kofar Kaura, Katsina, +2348025507003
INA mik'a sak'on ta’aziyya ga’yan’uwa da abokan
sana’ar marigayiya Jamila Haruna. Allah Ya jik'an ta, Ya kuma
sa Aljanna ce makomar ta. Allah kuma Ya albarkaci abin da ta bari.
SAKO GA SHEHU KANO
Daga Garba A.
Nuhu,
Mariga, Jihar Neja,
+2347085226577
INA mik'a sak'on gaisuwa ga ]aukacin masu sana’ar Fim. Ina
kuma yi maku addu’ar fatan alheri a ko da yaushe. Allah Ya
taimake ku a kan wannan sana’a. Sannan ina kira ga Shehu Hassan
Kano da cewa in an
girma a san an girma. Kukan kurciya jawabi ne!
MU MA MUN SARA MATA
Daga Murtala A.
Jalingo,
+2348022735655
A GASKIYA irin rawar da mujallar Fim ta taka ba ma ’yan fim
kawai ya dace a ce sun sara mata ba, har da duk ma su karatu ya
dace su sara mata, tare da jinjina mata dangane da irin namijin
k'ok'arin da ta ke yi na nisha]antarwa da fa]akar da jama’a.
Jinjina ta musamman ga ma’aikatan ta, wa]anda su ke hana idon
su barci don kawai su gamsar da mu. Ina fatan Allah Ya sa ta ci
gaba da fitowa har k'arshen rayuwar mu. Allah kuma Ya kare shugabannin
ta da ma’aikatan ta daga sharrin masharranta. Jinjina ga Ibrahim
Sheme, Aliyu A. Gora II, da Sani Maikatanga.
’YAN FIM GA SHAWARA
Daga Amina Usman,
Numan, Jihar Adamawa.
+2348060616756
INA son edita’ya isar min da sak'on gyara ga kamfanin ‘Rainbow
CD Nig. Ltd’, da cewa fim ]in da su ka shirya mai sunan ‘Garin
Mu Da Zafi’ akwai kuskure. Domin wak'ar ta sha bamban da jigon
labarin. Wak'ar ta na magana a kan halin-ha’ula-in da ’yan
fim su ke ciki, yayin da fim ]in kuma ya k'are a kan soyayya. Shawara
ta ga masu shirya fim ita ce a cire son zuciya da tsoro a yi fim
mai inganci, wanda zai isar da sak'o, musamman a kan azzaluman ’yan
siyasar da su ka addabe mu a k'asar nan. Fatan alheri ga dukkan
’yan fim. Gaisuwa ta musamman ga ma’aikatan kamfanin
mujallar Fim.
DUBI DAI JAMILA HARUNA
Daga S. Dauda
Ahmad,
C.I.LS,
+2348068210162
INA fatan edita zai taimake ni ya isara sak'on tga’aziyya
ta ga ’yan’uwa da iyalan marigayiya Jamila Haruna. Allah
Ya jik'an ta da rahama. Hak'ik'a duniyar fim ]in Hausa gaba ]aya
mun yi babban rashi, domin Jamila ta na daga cikin matan fim masu
k'ok'arin ha~aka harshen Hausa da al’adu nagari. Duk inda
za ka gan ta za ka gan ta da k'unshi hannu da k'afa. Duk wanda ya
ke son ya tabbatar da haka ya nemi fim ]in ‘Sake’. Don
haka na ke kira ga sauran abokan sana’ar ta da cewa su yi
k'ok'arin koyi da Jamila Haruna, su ba da tasu gudummuwar wajen
ha~aka harshe da al’adun Hausa tun da sauran lokaci. Allah
Ya ba da ikon yin hakan, amin.
JAJE DA TA’AZIYYA
Daga Alhaji Sani
2-Effects,
Yauri, Jihar Kebbi.
08025161253
INA mik'a sak'on jaje ga Sani Musa Danja game da ha]arin mota da
ya rutsa da shi har ya karye. Da fatan Allah Ya ba shi lafiya. Sannan
ina mik'a sak'on ta’aziyya ga iyalan marigayiya Jamila Haruna.
Allah Ya gafarta mata zunuban ta, Ya sa kuma Aljanna ce makomar
ta. Mu kuma Allah Ya sa tamu ta zo mana da kyau.
ALLAH JIKAN RAI
Daga Abubakar
Musa Anka,
Jihar Zamfara,
08025301572
A MADADIN kamfanin AnkaMotion Pictures, ina yi wa ilahirin ’yan
fim da sauran Musulmi ta’aziyyar Jamila Haruna. Allah Ya gafarta
mata tare da sauran Musulmin da su ka riga mu gidan gaskiya. Sani
Danja kuma da sauran marasa lafiya, Allah Ya ba su lafiya.
AIKIN KU YA YI KYAU
Daga Abubakar
Saddiq,
No. 47, Magajin Rafi Road, Birnin Kebbi.
+2347030304744, +2348020696066
GAISUWA ga ma’aikatan mujallar Fim. Fim ta cancanci a yaba
mata, ba don komai ba sai don tsage gaskiya komai ]acin ta. Aikin
ku ya yi kyau. Allah Ya k'ara kare ku daga sharrin rayuwa, Ya kuma
k'ara ]aukaka mujallar Fim ko da mahassada ba sa so. Gaisuwa ta
musamman ga Ibrahim Sheme, Alyu A. Gora II, Sani Maikatanga, Maimuna
Alhassan da sauran m a’aikatan mujallar Fim baki ]aya.
MATASHIYA GA UMMANCY
Daga Kabeer Sakaina,
Layin ‘Yangoro Malumfashi,
+234 802 649 9380, +234 703 976 9596
I-mel: kabeersakaina@gmail.com
DA fatan ki na lafiya amin. Hak'ik'a wannan fili naki na ‘Rayuwar
Iyali’, fili ne da zai rik'a wayar wa ]imbin matan Hausawa
da kai, musamman na karkara. Allah Ya ba ki ikon ci gaba da fa]akarwa
a kan gaskiya, amin.
Sharhin da ki ka yi mai taken “Finafinan da ya kamata mata
magidanta su rik'a kallo,” hak'ik'a ya yi, don ya zo a lokacin
da ]imbin mata magidanta ke buk'atar sanin abubuwan da ke sa ba
su iya lank'wasa mazajen su. Ya zo a daidai lokacin da mata magidanta
ke son sanin hanyoyin da za su iya gamsar da mazajen su a dukkannin
zaman auren su. Allah ya saka maki da alheri, amin. Zan so ki rik'a
yin cikakken bayani a cikin sharhin da ki ke yi, musamman wanda
ya shafi jima’i. Ina son ki san cewar mafiya yawan masu karatun
mujallar Fim mata ne, kuma matan aure, wa]anda su ke zaune a gidan
mazajen su. Za su iya yin amfani da dukkan abubuwan da aka rubuta,
musamman a wannan fili naki. Haka kuma akwai matan da ba su iya
karatu ba sai dai su taru a rik'a karanta masu don su ma su na son
cin moriyar wannan fili naki.
A cikin sharhin ki inda ki ka ba da misali da irin finafinan da
ya kamata mata magidanta su rik'a kallo, inda ki ka ce finafinai
da soyayya tsagwaron ta ga miji da kuma koyon kisisina da kissa
da kuma kwanciya irin ta jima’i, finafinai ne da su ke da
matuk'ar tasiri ga duk wata macen da ke buk'atar auren ta ya ]ore.
Ummancy don Allah ki yi tunanin yadda al’ummar Hausawa, musamman
matan karkara, za su fassara wannan nuni da ki ka yi masu. Sannan
ki yi tunanin yadda mafiya yawan masu karatu za su fassara kallon
fim na kwanciyar jima’i da kallon fim na nuna tsiraici. Sannan
ki tuna da yadda addinin mu ya haramta mana kallon tsiraicin junan
mu.
Ba lallai ba ne wannan fassara da na yi maki ta zamo ita ce hak'ik'anin
abin da ki ke nufi. Zan so ki k'ara yin bayani filla-filla don kauce
wa gur~atacciyar fassara ga al’umma, don gudun kada a k'ok'arin
neman lada a samo zunubi, kada a k'ok'arin fa]akar da al’umma
daidai a jefa su ga halaka. Idan har ki na nufin kallon finafinan
nuna tsiraici don koyon yadda ake kwanciyar gamsar da miji ga mata,
to ina fatan za ki gyara wannan tunanin naki. Don akwai hanyoyin
kwanciyar iyali kala-kala wadda ba ta sa~a wa addinin mu ba. Idan
kuwa akwai abin da ki ke nufi, to ki k'ara warware wannan bayani
naki don sak'on da ake son isarwa ya isa inda aka aike shi. Warware
wannan bayani naki filla-filla shi zai ba mata magidanta samun damar
cin moriyar wannan filin. Allah Ya ba ki ikon yin bayanin da zai
ceto matan Hausawa daga fa]awa tarkon da ya ke koro su daga gidajen
mazajen su, amin.
‘BOLANLE’ SHIRME NE
Daga Maryam Salis,
Malali, Kaduna.
+2348020529413
DON Allah edita ka ba ni ]an fili a cikin wannan mujalla mai tarin
albarka domin in isar da sak'on gyara ga kamfanin 2-Effects game
da album ]in su da su ka saki mai suna ‘Bolanle’.Wallahi
saboda takaici har sai da na zubar da kofin shayi na da na kalle
shi. Domin a gaskiya babu wani abin birgewa a cikin sa ban da shirme.
Wannan shi ake ce wa ana so a yi Bature ba a iya ba, inji Bayarbe
da ya ga Zabaya. A gaskiya gara ma su tsaya a kan irin wak'ok'in
da aka fi sanin su da su na fim. Da fatan za su ]auki shawara ta.
KU HADA NI DA ALI NUHU
Daga Cpl. Abubakar
Mohammed,
Nigeria Police Force, Malali Division,
Kaduna.
+234 8082414229
INA mai mik'a sak'on ta’aziyya ga mawalafin wannan mujalla
mai tarin albarka, wato Malam Ibrahim Sheme, dangane da rashin matar
sa Hajiya Binta da ya yi. Allah Ya sa Aljannah Firdausi ce makomar
ta. Mu kuma Allah Ya kyautata namu k'arshen.
Ina so ku ha]ani da shahararren ]an wasa, wato jarumi Ali Nuhu,
domin ina son abokantaka da shi. Allah Ya ja zamanin mujallar Fim
da ma’aikatan ta. Gaisuwa ga dukkan ’yan fim.
RASHIN YA SHAFI KOWA
Daga Yahya Easy,
Bakin Kura, Jihar Bauci
DA farko ina mik'a sak'on gaisuwa da jinjina ga mujallar Fim da
]aukacin ma’aikatan ta. Bayan haka ina son edita ya mik'a
sak'on gaisuwar ta’aziyya ta ga Malam Ibrahim Sheme dangane
da rasuwar matar sa. Wannan rashi ba shi ka]ai aka yi ma wa ba,
har da k'asa baki ]aya a matsayin ta na k'wararrar mai ilimantar
da jama’a. Allah Ya jik'an ta da gafara. Shi kuma Ibrahim
Sheme Allah Ya ba shi hak'urin wannan babban rashi. Allah Ya sa
mu cika da kyau da imani.
ALLAH YA BA SANI LAFIYA
Daga Femi Danyaro,
B.C.G.A, Malumfashi Jihar Katsina,
+2348065584699
INA fatan edita zai ba ni dama in mik'a sak'on gaisuwa da jaje
ga jarumi Sani Musa Danja game da ha]arin mota da ya rutsa da shi.
Mu na taya shi addu’ar Allah Ya ba shi lafiya. Jinjina ta
musamman ga Ibrahim Sheme, Aliyu A. Gora II, da Sani Maikatanga.
Allah Ya k'ara maku basira.
SAKON TA’AZIYYA
Daga Naseer Danhutu,
Wanka, Jihar Bauchi,
+2347034773393
INA rok'on edita ya ba ni dama ni ma in mik'a sak'on ta’aziyya
dangane da rasuwar Malama Binta, wato matar Alhaji Ibrahim Sheme.
Allah Ya ba iyalai da ’yan’uwa hak'urin jure wannan
babban rashi. Allah Ya ha]a mu da ita a Aljannah ma]aukakiya. Gaisuwa
ga dukkan ma’aikatan mujallar Fim.
FATI NIJAR TA BIRGE NI
Daga Abubakar
Saddiq,
No. 47, Magajin Rafi Road, Birnin Kebbi.
+2347030304744, +2348020696066
INA fata edita zai ba ni fili a cikin wannan mujalla mai farin
jini da albarka in isar da sak'on gaisuwa da jinjina ga Fati Nijar.
Ina shaida maki cewa a gaskiya kin birge ni da ki ka halarci bikin
auren Ali Jita. Duk da cewa kun yi soyayya da shi amma kishi bai
hana ki zuwa ba. Allah Ya saka maki da alheri, Ya kuma ba ki miji
nagari.
GAISUWA GA MA’AURATA
Daga Walidah M.
Barde,
Badagry, Jihar Legas.
+2348024601301
EDITA ka ba ni fili in mik'a sak'on ta’aziyyar marigayiya
Jamila Haruna. Allah Ya jik'an ta da gafara, Ya sa Aljannah ce makomar
ta. Mu kuma Allah Ya sa mu cika da imani. Ina kuma mik'a sak'on
taya murna ga dukkan ’yan fim da su ka yi aure a ’yan
watannin baya. Gaisuwa ga Hadiza Maina, Naziru Ahmed, Binta I.S.I.
Abubakar Ibiyoyi, Aminu Saira, Awwal Isah West, da kuma darakta
Saminu M. Mahmud. A gaida ma’aikatan mujallar Fim maza da
mata.
KU DAINA LA’ANTAR SU
Daga Madu
Abbatuwa, Agege Legas,
+2348023841075
TARE da sallama irin ta addinin Musulunci. Bayan haka ina son edita
ya ba ni dama in yi tsokaci a kan irin mutanen nan da ke la’antar
’yan fim ba tare da wata k'ak'k'warar hujja ba. Duk da la’antar
da ku ke yi masu, sai ga shi Allah Ya kawo mu lokacin da su ke ta
aure su na kuma zama a gidajen mazan su har su ka zama abin sha’awa.
Ina son in jawo hankalin irin wa]annan mutanen da cewa idan ba za
ka yi wa mutum nasiha ba a kan wani abu da ka ke ganin ba daidai
ba ne, to ka kama bakin ka ka daina la’antar sa tunda rayuwar
sa ba a hannun ka ta ke ba. Da fatan an gamsu. Gaisuwa ga mawallafiyar
mujallar Fim Hajiya Maryam, da Ibrahim Sheme, Aliyu A. Gora II,
Sani Maikatanga, Maimuna Alhassan, da sauran ma’aikatan mujallar
Fim baki ]aya.
KI NA FA DA AURE!
Daga Adam A. Adam,
Agege, Legas,
08066344755
DON Allah edita ka taimake ni da fili in isar da sak'on ta’aziyya
ga dukkan’yan fim dangane da rasuwar jaruma Hajiya Jamila
Haruna. Allah Ya jik'an ta da rahama.
Zan kuma yi amfani da wannan dama in taya gwani na Sani Danja addu’ar
Allah Ya ba shi lafiya. Ina kuma yi wa Mansura Isah nasiha da cewa
ta tuna fa akwai aure a kan ta. A gaskiya abubuwan da ta ke yi a
wajen biki in ta je ba su dace da ita ba. Ku fa ’yan fim ina
so ku sani cewa ku wakilai ne ga dukkan Hausawa. Duk abin da ku
ka yi haka duniya za ta ]auka cewa halayyar Bahaushe kenan. Da fatan
za a gyara. Allah Ya k'ara ha]a kan ku.
RABO MAYAUDARI NE
Daga Nuhu S. Aliyu
FK,
Tudun Nufawa, Kaduna.
+2348025238838
INA fatan Edita zai ba ni dama in isar da sak'o ga Malam Rabo.
Ina son Rabo ya tuna da cewa duk fa abin da ya yi farko, to zai
yi k'arshe. Ya daina tak'ama da ]aurin gindin da Shekarau ya ke
yi masa. Wallahi a lokacin da hak'k'in jama’a zai fara tambayar
sa Shekarau ba zai iya taimakon sa ba da amsa ba. Ni na tabbatar
da cewa Rabo da kan sa ya san ya na yaudarar Musulmi ne. Kuma mu
tsakanin mu da shi Allah Ya isa. Kuma abin da ya ke yi zubar wa
Musulunci mutunci ya ke yi. In ba yaudara ba, ya za a yi shi da
ya ke ik'irarin Musulunci, amma har yau babu wani mai laifi da su
ka ta~a yanke wa hukunci a kotun shari’ar Musulunci. Mun yarda
a yi gyara, amma me ya sa ake rufe shagunan sayar da finafinai,
amma har yanzu sinimomin da ke Kano kullum sai an nuna fim a cikin
su? Kai, mu mun gaji da da gafara sa ba mu ga k'aho ba. Kai dai
Rabo ka nemi ku]in ka tunda banza ta samu. Amma ka daina ra~ewa
da Musulunci ka na yaudarar Musulmi.
ALLAH JIKAN SU
Daga Umar Mariga,
Jihar Neja.
+2348026994546
INA son wannan mujalla mai farin jini tare da tarin albarka ta
ba ni dama in isar da sak'on ta’aziyya ga Ibrahim Sheme game
da rasuwar matar sa Hajiya Binta. Allah Ya jik'an ta, Ya sa ta huta.
Allah Ya jik'an Jamila Haruna da rahama, Ya sa ta huta. Allah kuma
Ya ba Sani Danja lafiya.
TAHIR DA BINTA INA MURNA
Daga Mrs Sa’adat
Yahaya,
Suleja, Jihar Neja.
+2348038289271
DON Allah Edita ka mik'a sak'on taya murna ta ga Binta I.S.I. da
maigidan ta Tahir I. Tahir game da auren da su ka yi. Allah Ya ba
su zaman lafiya. Ina kuma jajanta wa Sani Danja a kan abin da ya
same shi na ha]arin mota. Allah Ya ba shi lafiya, Ya kuma kyauta
gaba. A k'arshe ina mik'a gaisuwa ta ga iyayen Iman, Anty Hafsat
Izom, da kuma Yakubu da matar sa.
A GAIDA NAKWANGO
Daga Haruna Galadima,
Jihar Adamawa.
+2348088844448
EDITA ina son ka ba ni fili domin in isar da gaisuwa ta musamman
ga dattijo Malam Kabiru Nakwango. Na jinjina masa kan irin yadda
ya ke fitowa a finafinan sa, musamman fannin uba. Allah Ya k'ara
masa basira. A gaida dukkan ma’aikatan mujallar Fim.
FANTIMOTI GA GYARA
Daga Bello BG,
Gidan Madi, Jihar Sokoto.
+2348060037979, +2348022186767
DA fatan Edita zai ba ni fili domin in mik'a sak'on taya murna
ta ga A’isha Abaab dangane da auren ta da Abdurrahman Ibrahim.
Allah Ya ba su zaman lafiya. Ya kuma k'ara ha]a hankalin su da kuma
hak'uri da juna. Sannan zan yi amfani da wannan dama in yi kira
ga mawak'iyar nan Maryam Fantimoti dangane da wak'ar da ta yi ta
‘Jigida’. Kalmomin da ta yi amfani da su wajen wak'ar
sam ba su dace ba. Saboda kalmomin batsa ne k'arara, wa]anda ba
zan iya fa]ar su ba. Ina son ta sani cewa akwai ]imbin jama’a
masoyan ta masu sauraren wak'ok'in ta maza da mata. Don haka ina
k'ara ba ta shawara a kan ta rik'a tace duk wani album da za ta
fitar a kasuwa domin amfanin jama’a.
NA GA ALFANUN FIM
Daga Kabir Maldini,
Numan, Jihar Adamawa.
SABODA mujallar Fim aka yi min abin da ba zan ta~a mantawa da shi
ba a rayuwa ta. Wato na shigo mota daga Kano zan koma garin mu Adamawa.
Tashin mu ke da wuya, tun ba mu yi nisa ba sai motar mu ta fara
ba mu matsala. A tak'aice dai sai k'arfe 8:00 na dare mu ka isa
Gombe. Nan take direban ya ce ba zai k'arasa ba sai cikin dare ko
in gari ya waye saboda hanyar ba ta da kyau. Haka dai kowa ya hak'ura.
Sai na tuna ina da aboki a Gombe mai suna Nura Muhammad. Ya na Bolari
ne da zama. Sanadiyyar mujallar Fim mu ka saba da shi tamkar da
ma mun san juna. Nan take na kira shi a waya. Ya ce, “Yaya
gida?” Na ce, “Ai ina Gombe.” Ya ce, “Lafiya?”
Na ce ga dalili kuma ga inda mu ke. Ya nuna damuwar sa matuk'a a
kan lamarin. A tak'aice dai gidan su ya kai ni na kwana. Su ka mutunta
ni sosai. Ba abin da zan ce masa sai dai godiya da fatan alheri
ga iyayen sa. Allah Ya saka masu da alheri. |