TASKUN DA KANANAN ZAWARAWA SU KE FUSKANTA
DAGA UMMANCY UMAR
I-mel: ummancyumar@gmail.com
RAYUWAR IYALI
BAZAWARA dai ita ce macen da ta tab'a yin aure kuma auren ya mutu.
Mutuwar auren nan kuwa ko da wacce irin sanadiyyar ya zo har mijin
ta ya sake ta ko kuwa ita da kan ta ne ta nemi sakin. Daga lokacin
da ta kammala iddar ta idan Musulma ce ta zama bazawara.
Mace ta kan iya zama bazawara ko da kuwa mijin da ta aura bai sadu
da ita ba ajalin auren nasu ya cika, duk da yake da akwai masu ganin
cewa muddin dai mace ba ta sadu da mijin ta ba har auren ya mutu
ba ta zama bazawara ba, da dai a ce mata ta tab'a yin aure. Ko ma
da wacce fassara mutum ya d'auka a d'ayan biyu, bazawara dai ita
ce matar da ta tab'a yin aure.
Shi dai aure abu ne wanda a duk lokacin da aka d'aura shi ake fata
da kuma burin ganin ma’aurata sun yi zaman mutu-ka-raba ne,
amma kuma duk da irin wannan fatar da ma’aurata, ’yan’uwan
su abokan arziki da kuma iyaye su ke da shi, idan har ajalin mutuwar
zaman aure ya zo tabbas sai an rabu; sai dai kuma idan da rabon
ma’auratan su sake dawowa da zama a matsayin miji da mata
Allah Ya na iya sake had'awa.
Kamar yadda mutuwa ta ke d'aukar duk wanda kwanan sa ya k'are,
babu babba babu yaro babu tsoho babu matashi, haka shi kan sa ajali
na aure yake, idan ya tashi kawo k'arshen zama babu ruwan sa da
shekaru ko mulki ko muk'amin da ma'auratan su ke da shi, kawai shiga
yake ya katse igiyar auren.
Kamar yadda idan ajali ya zo ko babu ciwo a mace, haka shi ma ajali
na aure yake, wani lokacin ya kan faru ne haka kawai ba tare da
wasu ko wani dalili mai k'arfi ba. Wani lokacin kuwa ya na faruwa
ne saboda sakacin da mara lafiya ya ke yi wajen k'in kula da bin
shawarwarin da likita ya ba shi tun lokacin da aka gano ya na da
matsala, to shi ma haka ajalin zaman aure ya ke. Sau tari ma’aurata
na k'in bin shawarar da magabatan su su ke ba su ne domin a samu
zaman aure mai inganici.
Kamar yadda wani lokacin mara lafiya ya ke d'aukar lokaci ya na
jinya, wani lokacin ma har ya kai shi ga kwanciya a asibiti, daga
bisani kuma ya mace, haka shi ma zaman aure ya ke. Wani lokacin
da zarar an yi aure, to fa zama babu dad'i, yau ana gaban wannan
ana sasantawa gobe ana gaban wancan. Wani lokacin ma sai ta kai
ga mace ta yi yajin da za ta k'aurace wa gidan mijin nata, daga
bisani kuma auren ya mace.
Idan mu ka duba, za mu ga cewa zaman aure da mutuwar aure su na
kama da ajali na mutuwa a wani lokaci, amma kuma da akwai inda su
ke da bambanci, domin ita mutuwa ba ta da magani kwata-kwata, amma
ita mutuwar aure ta na da magani; idan har aka kiyaye wasu abubuwa
ana iya samun tsawon rayuwa ta aure, amma idan kuma aka yi masa
sakaci irin na mai fama da ciwon hawan jini ko ciwon siga ko kuma
sida, nan ta ke mutuwa ta na iya zuwa ta tauke shi.
Duk wani mai fama da ciwon siga, hawan jini ko sida ya na da wuya
ki ga cewa ya na wasa da duk wata shawara da likita zai ba shi domin
gudun kada mutuwa ta yi awon gaba da shi. Masu irin wannan ciwon
kullum su na cikin motsa jiki da kuma gudun cin duk wani abu da
likita ya hana su ci tare kuma da shan magani a daidai lokacin da
likita ya umurce su. Don haka su ke samun kuzari na tsawon lokaci
kafin mutuwa ta zo ta d'auke su.
Wannan duk shimfid'a ce ta yadda sakaci da kuma rashin bai wa ’ya’ya
mata mazajen da su ka dace da su da kuma lokacin da ya kamata mu
ba da su saboda yanayin zamani ya jawo karin k'ananan zawarawa da
auren su ya ke mutuwa a kowace rana ta Allah, kuma har yanzun nan
iyaye ba su fuskanci zurfin matsalar da irin wad'annan k'ananan
sauta-da-wawa su ke fuskanta ba da kuma bala’in da su ke k'ara
kawowa ga al’umma domin su kawo k'arshen wannan abin, don
haka kullum abin kamar k'aruwa ya ke yi.
A shekarun baya, idan har miji ya yi sakacin sakin matar sa mai
k'arancin shekaru, ko da laifin ta ko ba laifin ta, to tabbas sai
ya ga takaici, domin kafin ma ta gaba idda mazaje da dama su na
jiran ta. Don haka ne ma ake kiran duk wanda ya saki mace mai k'arancin
shekaru wawa, ita kuwa wacce aka sakar ake ce mata sauta-ga-wawa.
A wannan lokacin ya na da matuk'ar wahalar gaske ki ga mace ’yar
shekaru 16 zuwa 20 an sake ta, ko da kuwa mijin ta ya na fuskantar
matsalar zama da ita. Haka kuma idan har ma an saki mata masu irin
wannan shekaru, tabbas sai an samu cewa ta d'an jima a gidan miji
ba wai ta yi zama na d'an wasu watanni ne ko shekarun ba a gidan
mijin ba.
Irin wad'annan zawarawan a wancan lokacin ana samun su da kamun
kai, domin wata daga ranar da auren ta ya mutu har zuwa lokacin
yin wani auren nata ba za a gan ta a waje ko a titi ya na yawo unguwa
unguwa ba. Wannan ya sa har k'aramar bazawara, har ma da manyan
zawarawan wannan zamanin na da bayan an sake su har su yi wani aure
ba kowa ya sani ba. Sai dai kawai tsoffin mata da su ke unguwanni
ne su ke sani, su ma ganin su ne neman ma wasu mazan zawarawa ne.
Don haka duk gidan da aure ya mace a kunnen su, amma ba wai mace
idan auren ta ya mutu a gan ta a titi ta na tallar kan ta ba.
A yau, iyaye sun maida ’ya’yan su haja, duk wanda ya
zo ya taya. Idan yana tayawa da maik'o ko an gan shi da alamun mai
hannu da shuni ne a ba shi. A yau iyaye burin su shi ne su aurar
da ’yar su ga duk wanda ya nuna sha’awar sa ba tare
da binciken asalin sa da yanayin iya rik'e masu da kare mutuncin
’yar su ba. A yau iyaye sun k'yale ’ya’yan su
su na da k'arfi da ’yancin zab'ar wa kan su mazajen da za
su aura ba tare da ba su shawara ko cusa masu tarbiyyar ’ya’yan
su, su sukar masu dukkan ragamar rayuwar su ba.
A yau burin iyaye shi ne su dai su aurar da ’yar su ba tare
da ba ta tarbiyya ko ilimin addini da na zamani ba. A yau ya na
da matuk'ar wahalar gaske ki samu iyayen da za su aurar da ’yar
su su zaunar da ita su na mata hud'uba ak'alla na watanni uku kafin
zuwan aure domin su karantar da ita yadda rayuwar zaman aure ya
ke.
Wad'annan matsalolin da wasu da dama su ne zan kawo muku su idan
Allah Ya kai mu fitowa ta gaba domin ganin abin a zahiri yadda iyaye
su ke yin sakaci wajen aurar ta ’ya’yan su mata wanda
daga bisani kuma bayan namiji ya b'are ta, ya kwad'aita mata sanin
dad'in namiji, ya bambanta mata tsakanin ’ya mace da mace,
ya sauya mata fasali, ya kwantar mata da nonuwan da aka aurar masa
ita da su a tsaitsaye, daga bisani ya ingiza k'yeyar ta, wanda hakan
kuma ya sa idan ta dawo gida ta rik'a ganin da ita da uwar ta duk
d'aya su ke. Su kuma samari na unguwa da kuma alhazan banza su yi
yunk'urin maida ita filin sauke sha’awar su.
Sai dai kuma kafin wannan lokacin, ina son iyaye su yi karatun
ta-natsu musamman ga wad'anda ba su riga sun aurar da ’ya’yan
su domin ganin cewa masu neman ’ya’yan su da aure ba
wad'anda za su sako su ba ne bayan ’yan lokuta na zaman aure.
Su kuwa iyayen da aka riga aka sako nasu ’ya’ya, su
yi nazarin kuskuren da su ka yi domin kauce wa aukuwar hakan nan
gaba. |