BAYANI KAN SHA’AWA (2)
DAGA NABEELA IBRAHEEM
KHALEEL
DAGA ZUCIYA
ASSALAMU alaikum. Ina mana barka da sake saduwa a cikin wannan
fili. Allah Ya sa mu kasance cikin kulawar Sa a koda yaushe, amin.
In sha Allah zan ci gaba da bayani kan sha’awa. Ga wad'anda
su ka aiko da k'arin tambayoyi kan sha’awa, in shaAllah za
su ga amsar tambayoyin su a bayanin da zai biyo baya.
YADDA SHA’AWAR D'A NAMIJI TA KE
Yanayin sha’awar d'a namiji ta kasance mai girma kuma mai
k'arfi k'warai. Ta kasance mai saurin motsawa kuma koda yaushe kusa-kusa
ta ke. Dalilin hakan shi ne domin sinadarin sha'awar nan, watau
testosterone, ya kasance kuma shi ne sinadarin da ke tabbatar da
jinsin namiji. In har jikin d'a namiji ya samu matsalar sarrafa
sinadarin testosterone, to namiji zai dinga girma a mace ne kawai.
Kasancewar sa sinadarin sha’awa kuma sinadarin mazantaka shi
ya sa sha’awar namiji ta fi ta ’ya mace yawa, saboda
ayyukan da ya ke a jikin d'a namiji ya ninka na mace da yawa. Tun
jariri na cikin uwar sa ake sakin sinadarin testosterone cikin jinin
sa domin ya mazantakar da k'wak'walwar sa. Shi ya sa k'wak'walwar
namij ta fi ta mace girma; haka ma wasu manyan namomin jiki irin
su huhu, anta, da sauran su. Haka kuma wannan sinadari shi ke kula
da girma da nunar k'ashi da jijiyoyi, shi ya sa k'arfin d'a namiji
ya fi na d'iya mace. Yawan sha’awar d'a namiji ta bambanta
daga mutum zuwa wani, daga wannan k'abila zuwa wata, sannan daga
k'asa zuwa k'asa. Sannan irin tasowar da mutum ya yi da yanayin
zafi ko sanyi na ruhin sa, da yanayin da ya ke cikin rayuwa duk
su na taka muhimmiyyar rawa ga yawa ko k'arancin sha’awa.
Abubuwa masu k'ara sha’awa su na matsanancin motsa (misali:
irin na sojoji), yanayi na tsananin farin ciki ko bak'in ciki. A
tak'aice dai ba wani abu mai k'ara yawan sha’awa na dindindin,
amma masu sa k'arancin sha’awa sun had'a da: Kasancewa cikin
tsananin huzni a ko da yaushe; matsananciyar gajiya ko takura, dannewar
mulki ko ikon mazantaka ko wani ciwo da zai sa jiki ya kasa sarrafa
sinadarin sha’awa. Haka ma nuna halin ko-in-kula daga gun
matar mutum; matsananciyar rama; k'iba mai tsanani da rashin cin
lafiyayyen abinci duk su na kawo k'arancin sha’awa. Sannan
tsufa ma ya na rage yawan sinadarin sha’awar da ake sarrafawa.
YANAYIN SHA'’AWAR ’YA MACE
Sha’awar ’ya mace ta kasance ’yar kad'an bisa
ga ta d'a namiji, domin dai sinadarin testosterone d'an kad'an ake
sarrafawa a jikin ta. Shi kuma sinadarin ’ya mace bai motso
sha’awa, iyaka dai ya sa mata tsananin son yin ibadar aure
ba don komai ba sai don ta samu ciki, domin wannan sinanari ya kasance
shi ke tabbatar da duk wata siffa da halayya ta ’ya mace,
babban al’amari daga cikin su kuwa shi ne d' aukar ciki da
haihuwa. Duk da cewa sinadarin sha’awar mace kad'an ne, amma
kuma sinadarin ya fi kaifi a jikin ’ya mace. Kusan abubuwan
da ke sa k'arancin sha’awa ga namiji su ke sawa ga mace ma,
sai dai ita in ta tsufa kwata-kwata jikin ta na daina sarrafa sinadarin
sha’awa da ma nata na ’ya mace. Sannan yawanci mata
sha’awar su na duk lokacin da su ka k'arato kwanakin hailar
su ko lokacin da su ke d'auke da juna biyu. Bambancin sha’awar
d'a namiji da ta d'iya mace: ta d'a namiji kamar kara ne da aka
kunna masa wuta; nan da nan zai kama gaba d'aya da k'arfin sa, haka
kuma nan da nan zai cinye ya zama toka; ta d'iya mace kuwa kamar
wutar ice ce; za ta fara ci kad'an, wata sa’a ma ta na mutuwa
sai an hura ta har ta yi k'arfi ta kuma dad'e ba ta mutu ba.
MAGANIN K'ARANCIN SHA’AWA
Mai fama da k'arancin sha’awa ya kamata ya fara gano abin
da ya haifar masa da wannan matsalar. Maganin k'arancin sha’awa
da aka samo daga Manzon Allah (SAW) da shi ne fate-faten alkama
da nama mai yawa. Sannan yawan cin ’ya’yan itatuwa,
musamman ma su ruwa-ruwa, kayan lambu, cin gasasshe ko dafaffen
nama, musamman na k'ananan dabbobi, da kuma yawan motsa jiki.
MAGANIN MATSANANCIYAR SHA’AWA
Kasancewa cikin matsananciyar sha’awa na nufi yawan sinadarin
sha’awan da ke cikin jini ya wuce yadda ya kamata. Abubuwa
da yawa na kawo haka. Muhimmai daga cikin su: ko dai mutum ya na
yin aikin k'arfi mai yawa kuma; kasancewa cikin tsananin huzni wanda
har ya rikitar da zuciya ta rink'a aikawa sa da sak'on da ba shi
ne ba ga k'wak'walwa, ko tsananin kwanciyar hankali da ta yi wa
mutum yawa, ga shi ko da yaushe cikin hutu; ko wani ciwo cikin namomin
jikin sa da ya haifar da k'aruwar sinadarin sha’awa, ko wata
qazamar halayya da mutum ya ke da ita da ke sa shi yawan tunane-tunane
na alfasha, ko kuma mutum mai cutar son mata, domin jikin sa ya
saba kullum cikin buk'atar sinadarin. Ya kamata mutum ya gano me
ke haifar masa da matsananciyar sha’awa, in na bari ne sai
ya bari. In bai aikin k'arfi da yawa sai ya fara, in ma ya na yi
sai ya k'ara, in k'wak'walwar sa ko da yaushe akwai abin da ke gaban
ta, a hankali za ta k'one kuzarin sha’awar da ya yi yawa.
Shi sa ya na da kyau mutum mai fama da matsananciyar sha’awa
ya tarkato aikin da bai son yi ko wanda ya ke ganin ya fi k'arfin
ya yi ta yi, a hankali zai fara son abin nan, domin kamar yadda
na fad'a a baya, ba kuzarin da ya kai kuzarin sha’awa k'arfi,
don haka in ya yi yawa ko in ba a amfani da shi ana iya juyar da
shi a cimma wani burin a rayuwa, maimakon a yi b'arnar sa wajen
bin mata ko a yi asarar sa haka nan a banza. Ya na da kyau mutum
mai fama da matsananciyar sha’awa ya durfafi tsayar da salla,
domin ta na hana alfasha, kamar yadda da yawa daga cikin ayoyin
K'ur’ani su ka nuna. Sannan zina, ko da a cikin zuciya kawai
ta faru, ta na d'aya daga cikin manyan alfasha. Sannan maganin sha’awa
da Annabi (SAW) ya koyar da mu shi ne yawan yin azumi a kai a kai,
wannan ya na rage yawan kuzarin jikin d'an’adam, kuma ya na
dakusar da sha’awa.
Zan dakata a nan. A wata na gaba in sha Allahu zan yi bayani kan
alak'ar sha’awa da soyayya da kuma bambancin soyayyar sha’awa
da ta ainihi, da ikkar soyayyar sha’awa kafin aure da bayan
auren. Allah Ya taimaka mana duka, amin.
|