’yan fim d'in. Hasali
ma wasu na ganin cewa yadda mazan su ka d'auki aure kamar sa hula
ne -- ka sa dara yau, gobe ka sa zanna. Ga matan kuma abin kamar
yin kitso ne, yau ki yi d'aure-d'aure gobe kuma a yi zane.
Masu karatu sun sha karantawa a shafukan wannan mujallar yadda
auratayya da mutuwar auratayyar 'yan fim ke kasancewa. Idan ba ku
manta ba a watannin baya mun kawo maku wani labari game da jarumar
nan fitacciya ta Nollywood, wato Stephanie Okereke, har ta shaida
mana cewa a kasuwa ta ke. Wata majiya mai k'arfi ta shaida mana
cewa a wannan lokacin jarumar su na kotu ne da mijin ta. Domin ita
jarumar ta rubuta takardar neman kotun da ta raba auren nata da
mijin ta, wani tsohon d'an wasan k'wallon k'afa na Super Eagles
wai shi Chikelue Illonyosi.
Jarumar, wadda ta tab'a shiga cikin jerin sunayen wad'anda su ka
sami nasarar shiga cikin gasar jarumar jarumai mata a gasar AMAA,
ta shaida wa majiyar mu cewa cin amana da yaudara na daga cikin
dalilan da take son kotu ta duba wajen raba wannan auren. Ita dai
wannan jarumar sun yi auren su ne a ciki Agusta 2004 a Legas. An
d'aura auren cikin rashin sanin cewar mijin nata na da wata matar
mai suna Ijeoma Mba a can Amerika. Kai, har ma da wasu ’yan
matan da ya ke nema barkatai. Ta k'ara da cewar a lokacin da ta
tuntub'i mijin nata kan wannan batun, bai mata musun hakan ba. Sai
dai wannan maganar ba ta yi masa dad'i ba domin maganar sai da ta
jawo ita jarumar ta sha na jaki a gun mijin.
A lokacin da Illonyosi ya ke maida martani kan zargin da Okereke
ke yi masa kan cewa ya yi mata sama da fad'i da wasu kayayyakin
ta, ya ce jarumar ta yo hayar wasu zauna gari banza wad'anda su
ka far wa gidan nasu su ka kuma yi awon gaba da kayayyakin sa. Ya
shaida wa kotu cewa zargin da jarumar ke yi masa na wai ta na bin
sa kayayyaki na miliyoyin naira da kuma batun ita ke kula da gida
da kuma d'aukar d'awainiyar gidan, duk zuk'i ta malle ce kawai.
Cikin k'orafin da ta mik'a wa kotu, Okereke ta buk'aci da kotu
ta umarci mijin da ya biya ta zunzurutun kud'i har naira miliyan
100 a matsayin diyyar wahalar da ta sha a sakamakon wannan watsi
da kuma yaudara da ya yi mata. Haka zalika ta buk'aci kotu da ta
umarce shi da ya dawo mata da wasu kayayyaki na mak'udan kud'i.
Sun had'a da mota Marsandi k'irar CLR 500 wadda aka k'iyasta za
ta kai naira miliyan uku da rabi, da kuma wata motar Baswaja Passat
2.0 mai lamba DP 182 GGE wadda ita ma aka k'iyasta za ta kai naira
miliyan uku da rabi. Akwai kuma komfuta laptop wadda za ta kai N150,000.
Sauran kayayyakin su had'a da firji, gas kuka, tukwane da wasu kayan,
wad'anda aka k'iyasta su kan N600,000. Cikin sauran kayayyakin da
jaruma ke son kotu ta karb'a mata akwai wasu karnuka gudu uku.
To amma duk da wannan badak'alar, Illonyosi ba ya son wannan rabuwar.
Amma kasancewar shari’a sab'anin hankali, daga k'arshe dai
kotu ta raba wannan auren. Stephanie Okereke dai an zama bazawara.
Da mujallar Fim ta tuntub'e ta ta waya a daidai lokacin da mu ke
daf da had'a wannan labarin a kan wannan al’amarin, sai jarumar
ta ce, “Gaskiya ban ji dad'i ba a ce aure na ya mutu cikin
k'ank'anin lokaci haka, to amma na koyi darasi. Ina kuma farin ciki
da wannan darasi da na koya. Ka ga nan gaba sai in yi taka-tsatsan
wajen zab'ar miji.” |