BABBAN LABARIN

LABARAI

An yi taron addu’a ga mamatan marubuta a Kano

RAN Lahadi, 7 ga Yuni 2009, ’ya’yan K'ungiyar Marubuta ta K'asa (ANA), reshen Jihar Kano, su ka yi taron tunawa da kuma addu’a da karatu na musamman ga ’yan’uwan su marubuta da su ka rasu. An shirya taron ne a d'akin taro na Murtala Muhammed da ke Kano. Da misalin k'arfe 10:00 na safe aka bud'e taro da addu’a, wanda Malam Sadi Mandawari ya yi.

Jawabin farko ya fito ne daga

bakin shugaban rik'o na k'ungiyar ta ANA, wato Dr. Yusuf Adamu, inda ya yi godiya da ’ya’yan k'ungiyar suka samu damar halartar taron. Bayan nan, sai shugaban taron, Farfesa Saleh Abdu, ya yi jawabi dangane da mamatan.

An gabatar da addu’o’i na musamman, wanda Malam Lawan Adamu Giginyu ya jagoranta, wato mawallafin mujallar ‘Zamani’. Har ila yau, samari sun gabatar da k'asidu da gajerun wak'ok'i ga wasu daga cikin ’ya’yan wannan k'ungiya su ka rubuta, kuma su ka karanta, wad'anda su ka shafi gudunmuwar su a fannin adabi.

An dai tashi daga taron lafiya da misalin k'arfe uku na yamma. Mamatan da aka yi wa wannan taro na musamman su ne Malama Binta S. Mohammed (wato maid'akin Ibrahim Sheme), da Abdullahi Muktar Yaron Malam, Abubakar Ishaq, Bashir Farouk Roukbah, da A’isha Usman Bugaje.

Wasu daga cikin wad'anda su ka halarci taron sun had'a da Bala Anas Babinlata, Badamasi S. Burji, Dr. Tanko, Dr. Hafizu Miko Yakasai, da dai sauran su. Malama Maryam Ali Ali ita ce wakiliyar shugaban ANA na k'asa a wurin.

 


 

 

’Yan fim na Katsina sun kai wa Rabo caffa

Daga SANI MAIKATANGA

RANAR Laraba, 10 ga Yuni 2009, ne shugabannin ’yan fim na Jihar Katsina su ka kai wa Darakta Janar na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Abubakar Rabo, ziyara a ofishin sa da ke Kano. Tawagar ta iso Kano da misalin k'arfe 2:00 na rana, a k'ark'ashin jagorancin babban sakataren k'ungiyar MOPPAN, reshen Jihar Katsina, Malam Abubakar Suleiman Saiwan. ’Yan tawagar sun had'a da mataimakin sakataren k'ungiyar, Malam Hamisu Lawal, sai Nana Garba, Abubakar Ayuba, da Isma’il Abba Masanawa, sai kuma shugaban k'ungiyar furodusoshi ta Jihar Katsina, Malam Rabi’u M. Yaro, da shugaban k'ungiyar daraktoci ta jihar, Mustapha B. Mohammed, Lawal Sa’idu, Hassan Isah, Kamal U.K. Soro, Jamilu S. Hameed, Abubakar M. Sadiq, Lawal Usman, da kuma Abdul’aziz A. Alibaba.

Jagoran tafiyar, Malam Abubakar Sulaiman, ya shaida wa wakilin mu cewa sun kawo ziyarar ne domin shimfid'a kyakkyawar dangataka da kuma mik'a wuya ga hukumar game da irin jagorancin da ta ke yi a k'ark'ashin jagorancin Malam Abubakar Rabo. Sai kuma neman alfarma a kan wata matsala da ta shafi wata ’yar wasa da yawancin furodusoshi su ka sa a finafinan su, amma aka nuna ba za a duba finafinan ba saboda jarumar ba ta yi rajista ba. “Duk da dai mun ji dai an ce ta yi, amma ba a kammala tantance ta ba. To a nan mu na neman alfarma da a taimaka mana a duba finafinan ’ya’yan mu. Kuma an yi hakan ne ba tare da sani ba. Amma nan gaba za mu duba mu tabbatar da duk wanda za mu sa a finafinan mu, sai mun tabbatar da ya na da shaidar kammala rajista da ita hukumar.

“Sannan mu na rok'on duk wani d'an mu ya zamanto ya nuna takarda daga wurin mu kafin a duba finafinan sa, don gudun samun matslala. Wanda yanzu haka mun taho da wad'annan takardun domin nuna wa ita wannan hukumar irin su.”

Jim kad'an bayan tattaunawar, sai tawagar ta isa ofishin Rabo. Bayan an bud'e taron da addu’a, sai aka ba su dama kowa ya gabatar da kan sa. Sannan aka saurari jawabin abin da ke tafe da su daga bakin Abubakar Suleiman. Bayan nan sai Malam Rabo ya gabatar da nasa jawabin.

Ya fara da yi wa sababbin shugabannin fatan alheiri. Ya yi kira da su sanya al’amurran da su ke yi a kan tsari na addini da al'ada mai kyau a cikin finafinan su. Ya kuma yi alk'awarin ba su goyon baya, da tabbatar da ci-gaba. Ya kuma sake shaida masu cewa, domin tabbatar da ci gaba da tsari mai kyau da ba da goyon baya ga masu shirya fim na Katsina.

Shugaban ya yi masu alk'awarin sa su a cikin tsari nataron k'ara wa juna sani (workshop) da hukumar za ta yi wa ’yan fim na Kano nan ba da dad'ewa ba. Ya buk'ace su da su ba da mutum biyu daga jihar su don shiga tsarin, amma idan har sun tabbatar da cika sharud'd'an da aka gindaya masu.

 

 

 

 

 


Kotu ta haramta wak'ok'in industiri guda 11

KOTUN ’yan fim, wadda ke k'ark'ashin Hukumar Tace Finafinai da D'ab’i ta Jihar Kano, ta haramta saurare ko yad'a wasu wak'ok'i guda 10 da ’yan fim su ka k'irk'ira a fad'in Jihar Kano.

Babban majistare Mukhtari Ahmed ne ya yanke wannan hukuncin a ranar 3 ga Yuni, 2009, tare da bayyana cewa haramcin ya fara aiki ba tare da b'ata lokaci ba.

Wak'ok'in da aka haramta d'in dai su ne:
1. “Hasbunallahu” ta su Aminu Ala
2. “Rabo-Rabo” ta Maryam A. Baba
3. “Sank'arau” ta Sa’id Ishaq Gobinda
4. “An Cuce Mu” ta Bello Billy
5. “Dawo-dawo” ta Nazifi Asnanic
6. “Jigida” ta Nazifi Asnanic
7. “Girgiza Kai” ta Naziru Hausawa
8. “Ibro Sauka a Mashin” ta ?
9. “Kukan Ibro” ta ?
10. “Kan Mai Uwa Da Wabi” ta Adam A. Zango
11. “Kowa Ya Ci Ubansa/Uwarsa” ta

A cewar alk'alin, wak'ok'in su na d'auke da batsa ne, da yak'ar hukuma, sannan sun sab'a wa tarbiyya tagari. Ya ce kotun za ta hukunta duk wanda aka samu ya na yad'a wak'ok'in, ko ya na sauraron su, ko ya na kwafar su daga wata na’ura.

Ya ce ya yanke wannan hukunci ne bisa tanajin Sashe na 97 na dokar da ta kafa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta shekarar 2001 da kuma dokar gidajen kallo ta dai ita wannan shekarar.

Alk'ali Ahmad ya bayyana cewa kamar yadda dokar ta tanada, duk wani mutum da aka kama ya na sayar da wani abin kallo ko na saurare ko na karantawa wanda ya k'unshi sab'o, tsiraici ko batsa da zai iya lalata tarbiyyar jama’a, to za a gurfanar da shi a gaban kotun.

Ban da haramta wak'ok'in da aka yi, jami’an hukumar sun kai samame a wasu kamfanonin buga wak'ok'i, amma ba su ci nasarar kama kowa ba.

Wani darakta da bai so a ambaci sunan sa ya yi kokwanton manufar hukumar kan haramcin sauraren wad'annan wak'ok'in. Ya ce, “Su hangen su hakan ne zai gyara tarbiyyar Musulmin Jihar Kano. Sai dai ga duk ma’abocin hankali, abin kamar an yi baya ba zani ne, domin daga cikin wak'ok'in da aka haramta d'in babu wak'ar Barmani Coge, babu ta Ali Makaho, babu ta Sani D'an Indo, Babu ta Mai Asharalle, Babu ta Makosa, babu ta Kerewa, babu ta Micheal Jackson ko Bob Marley.
“A b'angaren yayin rufe kamfanonin buga wak'ok'i da shagunan sayar da finafinai ma haka al’amarin yake. Domin duk rufe-rufen da ake yi har yau ba a rufe gidan sinima ko d'aya ba. Har yau su na nan su na gyaran tarbiyya da finafinan Turawa, Indiya, Canis da kuma na kudancin Nijeriya. Ga DSTV a kowane otal ko babban gida. Bahaushe ya ce da ma wargi wuri gare shi. Ana tsoron inna inji ’ya’yan mayya! Ashe dai ko Baba da Baban sa.”


 

 

 

 

AN ce idan lalacewa ta taso wa kare, sai ya daina cizo ya koma tunkuyi. Da alama Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta fara fuskantar k'arancin aikin yi dangane da kakkab'ar ’ya’yan kad'anyar da ta ke yi wa ’yan fim. A bayyane yake cewa duk wanda ya amsa sunan sa a cikin harkar fim a Kano, hukumar ta karya shi da k'arfin iko. ’Yan fim dai tun su na d'an iya tagazawa, har sun hak'ura, kowa ya kama gaban sa. Tun ana samun na kamawa har ta kai ga ba a ma ganin su ballantana maganar kamu ta taso. To kun san masu iya magana sun ce da zaman banza, gara aikin banza.

Tunda yake ana k'amfar ’yan fim, yanzu hukumar ta karkata akalar ta zuwa ga mawak'a. Sai dai wasu mawak'an sawun b'arawo su ka taka. A ranar Alhamis, 4 ga Yuni, 2009, kotun hukunta ’yan fim ta Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta yi wa mawak'a shiri na musamman, inda ta kai farmaki wuraren da ake buga wak'ok'i, har ta samu nasarar cafke wasu mawak'an, ta yi awon gaba da su. A ranar ne aka kulle kamfanin buga wak'ok'i na Hikima Multimedia da ke kan Zoo Road a nan Kano.
Bayanai a kan dalilin rufe kamfanin sun kasu gida biyu. Na farko dai an ce ma’aikatan su na zargin cewa a wurin ne aka buga wak'ar da ta fi kowace wak'a tayar masu da hankali, wato ‘Hasbunallahu’, wadda su Aminu Ala su ka yi. Kuma ta na d'aya daga cikin wak'ok'in da a yanzu haka aka haramta jin su a fad'in Jihar Kano. A wani b'angaren kuma aka ce sun rufe wajen ne saboda laifin rashin sabunta rajistar kamfanin.
Sai dai kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida mana, duk abin an yi shi ne saboda zargin a wurin ne aka buga ‘Hasbunallahu.’
A ranar Lahadi, 6 ga Yuni 2009, jami’an hukumar sun yi wa Hikima dirar mikiya tun da sanyin safiya. An ce sun je da k'wararrun masana komfuta, wad'anda aka yi amfani da su wajen binciken komfutocin da ke wajen, ana neman gano idan a wajen ne aka yi wak'ar. Amma haka su ka gama binciken su su ka bar wurin hannu rabbana. Sannan tun farkon zuwan jami’an, babu wanda su ka fara nema sai Aminu Ala, wanda kusan shi ne jagoran rukunin mawak'an na ‘Hasbunallahu’, kuma manajan kamfanin. A lokacin Ala ba ya nan. Don haka sai su ka nemi ganin Sani Salisu Yakasai, wanda ke rik'e da muk'amin manajan darakta na wurin, shi ma ba a same shi ba.

Ban da wannan, sai kuma masoya da abokan arzik'i su ka yi ta buga wa mawak'an waya su na gargad'in su da cewa kar su bari su yi tozali da jami’an Hukumar Tace Finafinan, domin kama su ake nema a yi. Wannan ya sa ganin mawak'an ya yi wa wakilan mu wuya don jin ta bakin su. Sai dai wakilin mu ya samu tattaunawa da su ta wayar GSM. Mutum na farko da ya fara samu, Bashir D'and'ago, ya ce lallai ya na da masaniya kan wannan dambarwar. “K'warai, ina sane. Mutane da dama sun kira ni ta waya su na gaya min an rufe Hikima saboda wak'ar Hasbunallahu.”

Kan zancen ’yar b'oyo da mawak'an su ka fara yi don gudun kamu, sai ya ce, “Ni ba wani b'oyo da na ke yi. Ina nan ina yawo a gari. Kuma duk mai nema na ya san inda zai gan ni, don ni ba b'oyayye ba ne a cikin garin Kano. Kuma yau duk wanda ya saurari rediyon Kano ya ji murya ta, mu na wani shiri har na tsawon awa d'aya.”

To amma me ya sa tun da can ba a kulle Hikima ba sai bayan wata wak'a da mawak'a fiye da 50 daga Kano su ka je Kaduna su ka yi, su na rok'on Darakta Janar na Hukumar Alhazai ta jihar, Alhaji Sani Lawan K'ofar Mata, ya tsaya masu takarar kujerar gwamna a zab'en 2011? Anya siyasa ba ta shiga cikin al’amarin nan ba kuwa? Adamu Kirfi, wanda ya na d'aya daga cikin mawak'an na ‘Hasbunallahu’, ya amsa wannan tambayar da cewa, “Kai ma ka san akwai siyasa a ciki, musamman ganin irin rungumar da mu mawak'a mu ka yi masa. Kuma ba ma mu ba, duk wanda ya san Sani Lawan a Kano zai yi masa abin da mu ka yi masa in ya na da hali. Domin Sani Lawan mutum ne mai tausayi da son taimakon jama’a. Don haka ni a fahimta ta, ana so ne a tab'o Sani Lawan, aka kuma lab'e da wak'ar ‘Hasbunallahu’.”
Yanzu menene abin yi?

“Ba mu da wani abin yi illa mu bi yadda dokar k'asa ta tsara na neman hak'k'i idan aka tauye wa mutum,” cewar Kirfi.

Shi kuwa uban tafiyar, wato Aminu Ala, mun tambaye shi, shin da ma ya na da masaniyar zuwan ma’aikatan ne, shi ya sa ya k'i zuwa ofis a ranar? Ya ce, “Ni da ma a lokacin ina kan hanya ta ta zuwa Katsina. Na bar wurin kenan aka ce sun zo. Waya aka yi min ana shaida min ga abubuwan da ke faruwa. Bayan na dawo kuma sai masoya su ka rik'a bugo min su na shaida min cewa in aka gan mu kama mu za a yi.”
Hikima dai kamfanin Alhaji Sani Lawan K'ofar Mata ne. Shi me ya ce dangane da al’amarin? Sai Ala ya ce, Wallahi tun da na shigo Kano na ke neman layin shi amma har yanzu ban same shi ba.”

Sai dai bincike ya nuna duk ruwan su na k'ok'arin k'arewa ne a kan Ala. Domin su kan su jami’an na Hukumar Tace Finafinan shi su ke son yin tozali da shi, ko me ya sa? “To, ni ma abin ya na d'aure min kai. An ce an dakatar da wak'ok'i har guda goma. Amma me ya sa ba a neman wad'anda su ka rera sauran wak'ok'in sai dai Aminu Ala kawai? Ka ga wannan abin tambaya ne,” cewar Ala. To ko dai akwai siyasa a cikin al’amarin? Mawak'in sai ya kada baki ya amsa da cewa, “Ba abin mamaki ba ne, musammana yadda su ka ga irin d'aukakar da Allah Ya yi wa shi Alhaji Sani Lawan d'in. Don haka in ma an ce akwai siyasa a ciki ni ba zan musa ba.”

Ko akwai matakin da mawak'an ke shirin d'auka game da wannan badak'ala? Misbahu M. Ahmad ya amsa tambayar da cewa, “Ai mu ba mu da wani mataki da za mu d'auka da ya wuce mu bar komai ga Allah. Idan mutum ya na jin giyar mulki ta na d'ibar sa ya na wulak'anta jama’a, wata rana ya na ji ya na gani sai dai ya ga ana yi. Mu mun dogara ga Allah, kuma za mu ci gaba da gaya wa Allah,
shi zai ba mu mafita.”

Wakilin mu ya yi iyakar k'ok'arin tattaunawa da Sani Salisu Yakasai, wato babban manajan Hikima Multimedia, don jin ta bakin sa, amma ya ce shi ba zai iya cewa komai ba. Abin da kawai ya sani shi ne an kulle
Hikima an kuma bud'e.

Wannan al’amari dai yanzu haka ya sanya mafi yawancin mawak'an barin mahaifar su zuwa gudun hijira a wasu garuruwan; wasu na Kaduna, wasu Jos, wasu Abuja. Kai, akwai ma wanda ya na tashi daga Kano ba inda ya zame sai Lokoja, inda ba ya da dangin uwa balle na uba. Ya naji ya na gani mahaifar sa ta gagare shi zama.

Wani abu da ya d'aure wa ’yan fim kai shi ne mafi yawancin mutanen da hukumar ke farauta su na daga cikin wad'anda su ka yi rajista da hukumar. Masu lura da al'amurran yau da kullum a fagen shirin fim sun sha hasashen cewa yin rajistar ba zai yi wani alfanu ba. In ba ku manta ba, a Fim ta watan Nuwamba 2008, mu ka bugo jerin sunayen ’yan fim da ake sa ran da d'ai d'ai da d'ai d'ai za a kama su. Har a wancan lokacin Ali Nuhu ya yi azarb'ab'in k'aryata mu a jaridar Sunday Trust ta ranar Lahadi, 16 ga Nuwamba 2008.

Sunayen da mu ka buga a wancan lokacin cewa wata k'wak'k'warar majiya ta shaida mana cewa Rabo na so ya kama su ne:
1. Ibrahim Mandawari
2. Sani Mu’azu
3. Ahmad Alkanawy
4. Ado Gidan Dabino
5. Saratu Gid'ad'o
6. Ali Nuhu
7. Sani Masu Danja
8. Falalu D'orayi
9. Naziru Hausawa
10. Aminu Ala
11. Dakta Ahmad Sarari
12. Rabi’u Ibrahim (Daushe)
13. Rabi’u Ibrahim (HRB)
14. Jamila Haruna Yakasai
15. Adam A. Zango
16. Kabiru Arayu
17. Maryam Sangandale
18. Balaraba Ramat Yakubu
19. Mamman Mutu-ka-raba
20. Abdulhadi Awilo
21. Isma’il I.U.I.
22. Maryam Fantimoti
23. Aminu Maidawayya
24. Aminu Bala (Mugu)
25. Bala Anas Babinlata
26. Aminu Ahmed (Saira)
27. Sadi Sidi Sharifai
28. Fati Nijar
29. Murja Baba
30. Rasheeda Adam
31. Ashiru Nagoma
32. Dakta Umar Faruk Jibril
A wancan lokacin, mun shaida maku cewa ba su kenan ba.

 

 

 

 

 

AN KAMA ALI JITA SABODA WAK'AR BIKI

Daga ALIYU A. GORA II

IN ta bi daga-daga, na k'urya ka sha kashi! Masu hankali da yawa daga cikin ’yan fim tuni su ka fahimci cewa kiran da ake yi masu na cewa su je su yi rajista da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da ke k'ark'ashin jagorancin Abubakar Rabo duk yaudara ce. Don haka yawanci su ka cika cika rigunan su da iska su ka canza gari. Wasu kuwa, tuni su ka mik'a wuya su ka amsa kiran, saboda sa ran za a iya d'aga masu k'afa su ci gaba da sana’ar su tunda sun yi biyayya. Ashe abin ba haka ya ke ba. Hasali ma dai, wasun su sun gane su kan su kiwon ragon layya ake yi masu, domin yin rajistar bai yi masu maganin abin da su ke jin tsoron ba.

Ali Jita, d'aya daga cikin mawak'a masu tashe, ya yi rajista da su Rabo, tare da amincewa da duk lokacin da ya yi sabuwar wak'a, zai kai wa hukumar su duba don tantancewa kafin ya sake ta, kamar yadda ita hukumar ta umurci mawak'an da su rik'a yi. To amma duk biyayyar da Ali ya yi ba ta taimake shi ba, domin a ranar Alhamis, 4 ga Yuni, 2009, kotun hukunta ’yan fim ta Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta kama mawak'in a kan wata wak'a da ya yi ta biki, ba ma ta fim ba. “Sun kama ni ne a kan wata wak'a ta biki da na yi. Kuma wak'ar ma ina da satifiket d'in da su su ka ba ni kafin in sake ta. Kuma na nuna masu satifiket d'in. To ka san su in su ka kama ka, ko ka na da gaskiya sai ka je can ka yi masu bayani,” inji Ali Jita a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin mu bayan an sako shi.

Da yawa ana ganin cewa jami’an Rabo sun yi wa Ali Jita kamun wulak'anci ne. Domin kamar yadda ya ce, “Sun kira ni ta waya ne, a lokacin ina tare da mata ta, mun fito daga unguwa zan kai ta gida. Da su ka kira ni, sai su ka ce su na situdiyo na, su na so in zo zan nuna masu wata takarda. Ina zuwa na tarar da ’yan sanda da bindigogi sun zagaye wajen. Su ka kama ni, su ka tafi da ni. Tun wajen k'arfe 3 (na yamma) har dare ina hannun su, kuma duk mata ta ta na tare da ni. To da zan kwana ma, sai alk'alin ya taimake ni ya zo cikin dare, k'arfe 9:00 na dare aka yi shari’ar. Ya yanke min hukuncin wata biyu a gidan yari ko in biya tarar N15,000. Sai na da biya su ka sake ni.” Ali ci gaba da bayyana cewa ya na ganin maganin wannan wulak'acin kawai shi ne ’yan fim su tattara su bar garin Kano in su na son su tsira da mutucin su. Ya ce shi ma ya na ganin zai gangara zuwa Kaduna ya samu wuri ya ci gaba da sana’ar sa tunda su na da gwamna mai son jama’a da adalci. A wani labarin kuma, duk da a ranar, wani fitaccen mawak'in, wato Aminu Maidawayya, shi ma ya tsallake rijiya da baya. Domin shi ma maridan Rabo sun kai masa hari, amma sai su ka yi rashin sa’a ba su same shi ba. Duk da haka an ce sun kulle masa ofis. Tun daga ranar wakilan mu su ke neman shi ta waya, amma har aka tafi buga wannan mujallar babu wanda ya ji d'uriyar sa ballantana a ji ta bakin sa.

 

 

 

 

 


INNA lillahi wa inna ilaihi raji’un! A ranar Litinin 1, ga Yuni 2009, ita ce ranar da shahararriyar jaruma Safiya Musa za ta iya kira bak'ar rana, domin a ranar ne ta yi rashin abin da ba za ta iya samun madadin sa ba har abada. A ranar ne Allah Ya yi wa mahaifiyar ta Malama Hadiza Musa Makka rasuwa a gidan su mai lamba 25, Badarawa Road, Unguwar Shanu, Kaduna, da misalin k'arfe 8:30 na dare.

Mama Hadiza ta rasu ne sanadiyyar ciwon tarin fuka (asthma) da na zuciya. Kafin rasuwar ta, marigayiyar sai da ta yi jinya a wani asibiti mai zaman kan sa mai suna Dana Clinic da ke tsohon filin jirgin sama na Kaduna har na tsawon mako d'aya. Bayan ta samu sauk'i an sallame ta da kwana shida sai kuma ciwon ya dawo mata. Aka sake d'aukar ta zuwa asibitin sojoji na ‘44’ da ke unguwar Badikko, kan hanyar zuwa Tudun Wada, Kaduna. A nan kuma kwanan ta d'aya kacal ta samu sauk'i, aka sallame ta, ta koma gida. Bayan kwana biyar da sallamar ta ne Allah Ya yi mata cikawa.

Amma duk bidirin da ake yi Safiya ba ta gari, sai dai aka kira ta aka shaida mata rasuwar.
Mama Hadiza ta rasu ta bar mijin ta Alhaji Musa Makka da ’ya’ya biyar -- namiji d'aya, sauran kuma duk mata. Daga cikin ’ya’yan, Safiya ce ta hud'u. Marigayiyar ta bar jikoki bakwai - maza uku mata hud'u.
Da yake cikin daren Litinin d'in ne ta rasu, ba a yi jana’izar ta ba sai da safiyar Talala, 2 ga Yuni. Da yake labarin bai shiga industiri da sauri ba, babu wani d'an fim da ya samu jana’izar. Sai dai daga baya ’yan fim sun yi ta yin jerin gwano zuwa yi wa Safiya da ’yan’uwan ta gaisuwa. Sun had'a da Ummi Nuhu, wadda ita ce ’yar fim da ta fara zuwa gidan, sai Ubale Wanke-wanke, wanda ya wakilci Sani Danja, da ya ke shi ma ya na kwance ba lafiya; Yakubu Muhammad, Ibrahim Maishunku, Rasheeda Adam, Yusuf Maina, A’isha Abubakar ZIAU, Jamilu Kocila, Abubakar Yerima, Yakubu Lere, Nura Mado, Kawu Kamfa, Isma’il Na’abba (Afakallahu), Abubakar Musa Anka, Nasiru Anchau, da Rabi’u Ibrahim HRB.

Allah ya gafar wa Malama Hadiza Musa Makka, amin summa amin.

 

 

 

 

 

D'AYA daga cikin al’amuran da takurawar da Hukumar Tace Finafinain ta Jihar Kano ta yi wa industiri ya haifar shi ne rikid'ar ’yan fim da dama. Da yawan su, musamman mawak'a, sun fito fili su na yin fayafaye (wato albums) su na sayarwa. Haka kuma wasu ’yan wasa sun zama mawak'a duk da yake ba a tab'a zaton za su zama mawak'an ba.

Babu ma kamar Ummi Ibrahim (Zee-Zee), kyakkyawar jaruma wadda ta jima ba a ji d'uriyar ta ba, tun daga dai labarin bikin kewayowar ranar haihuwar ta wanda mu ka ba ku a Fim ta Maris 2008. To, ana zaton wuta a mak'era sai ta tashi a masak'a. Zee-Zee ta zama zabiya! Wak'ar kuma ba ta Hausa ta koma yi ba, a’a irin wak'ok'in nan ne na Turanci irin na ’yan kudancin Nijeriya. A yanzu haka Zee-Zee ta nan ta na k'ok'arin fito da album d'in da ta yi a k'ark'ashin wani kamfani mallakar wasu Inyamirai a Legas mai suna Townsquare Music. An ce kamfanin mallakar fitaccen mawak'in nan ne d'an k'abilar Ibo mai suna Timaya.
Kwanan baya Zee-Zee, wadda ’yar shekara 24 ce, ta zo Kaduna inda ta ba Rediyon Nijeriya na Kaduna samfurin faifan ta don a rik'a sakawa don mutane su ji inda ta koma. Wakilin mu ya samu mallakar faifan, kuma ya saurarin wak'ok'i biyu da ke cikin sa.

Mujallar Fim ta tuntub'i Inyamiran da Zee-Zee ke huld'a da su, kuma sun yi mana bayani kan wannan album da Zee-Zee ta ke shirin fitarwa. Ta hanyar Inyamiran ne ma mu ka san cewa ashe sunan ta na yanka Zainab. Wato Zainab Ibrahim; yanzu sunan da za ta rik'a amfani da shi kenan, ba Ummi Ibrahim ba. Amma kuma sunan ta na harkar wak'a shi ne Zee-Zee.

A bayani da masu kamfanin da Zee-Zee za ta yi wak'ok'in k'ark'ashin su su ka ba mu, an nuna cewa mahaifin Zee-Zee Bafillace ne, yayin da mahaifiyar ta take Balarabiya. Haka kuma sun nuna cewa Zee-Zee ta na takardar shaidar karatu ta difloma a sashen kasuwanci (Business Administration) daga Jami'ar Bayero, Kano.

Zee-Zee dai har ta kammala rikodin wak'ok'in ta, kuma sun yi wak'ok'in ne tare da mawak'a irin su Weather man, Jonah D’ Monarch, 2solo na Dem Mama Records, Rha d’ Answer, da sauran su. A yanzu haka ta na shutin d'in wata wak'a wai ita “Janglover” a faifan bidiyo, inda Weatherman da Jonah D’ Monarch za su fito a ciki.

An fi sanin Zee-Zee da bin wak'ok'i a finafinan Hausa, don haka akwai alamun cewa wannan ba wani sabon abu ba ne. A cewar ta, za ta koma yin wasan fim bayan ta gama da wannan album d'in na Turanci. Za a k'addamar da album d'in a Legas da Kano, inji masu shirya mata faifan.

Zee-Zee za ta kasance Bahaushiya ta farko da ta yi album d'in Turanci irin na zamani. Idan kun tuna, Yakubu Muhammad da Sani Danja su ne na farko da su ka yi album d'in Turanci a cikin ’yan fim na Hausa, wato “Bolanle.”

Mun yi k'ok'arin jin ta bakin Zee-Zee kan wannan al’amari, amma abin ya ci tura. Inyamiran da take tare da su sun hana ta yin mu’amala ko magana da kowa. Wannan ya haifar da ji-ta-ji-a a industiri da bayan ta. Wasu na cewa Zee-Zee ta zama budurwar mawak'i Timaya ce, wai kullum ta na Legas a wurin sa. Wai za ma su yi aure. Wasu kuma na cewa Inyamiran za su yi amfani da ita ne don su sami kud'i, ganin cewa ita fitacciyar ’yar wasa ce a Arewa. Akwai kuma masu cewa ko kad'an harkar wak'ok'in ’yan Kudu da Zee-Zee ta koma bai dace da ita ba a matsayin ta na Bahaushiya kuma ’yar Musulmi.

 

 

 

 

 


ABIN ba wuya! Auren fitaccen makad'i/mawak'in industiri Rabi’u Dalle da mu ka ba ku labari a Fim a cikin 2008 ya yi albarka. Domin kuwa kyakkyawar amaryar ta Rabi’u, wato Zainab, ta haifa masa d'a namiji a ranar Asabar, 13 ga Yuni 2009, aka rad'a masa suna Umar Magadad.
Zainab ta haihu ne a Asibitin Malam Aminu Kano da ke birnin Kano. An yi bikin rad'in suna a unguwa Shagari Quarters a nan Kano. ’Yan’uwa da abokan arzik'i da dama sun halarci bikin sunan. An kuma yi ruguntsumin biki lafiya an tashi lafiya.

Allah ya raya Umar a cikin Musulunci. Mai jego kuma Allah ya k'ara mata lafiya.

 

 

 

 

 

Daga IRO MAMMAN

K'UNGIYAR Dillalan Littattafai, Kayan D'ab’i da na Wasanni, reshen Jihar Kano (Books, Stationary and Sports Dealers Association, BSSDA), ta soki Hukumar Tace Finafinai da D'ab’i ta Jihar Kano da yi mata barazana ta hanyar tilasta wa ’ya’yan ta biyan kud'in rajista, wad'anda ta ce sun sab'a wa doka.

A wajajen watan Maris na bana, hukumar ta tab'a rubuta k'ungiyar takarda inda ta buk'aci ’ya’yan ta da su je kowannen su ya yi rajista a hukumar, inda zai biya kud'i N3,000, sannan ita kuma k'ungiyar an ce ta biya N5,000 a kowace shekara.

To, sai k'ungiyar ta d'auki wani lauya, wanda ya jagorance su zuwa Majalisar Dokoki ta Jihar Kano don karb'o kwafe na kundin dokar da ta kafa hukumar. A nan ne su ka gano cewa ko kad'an hukumar ba ta hurumin yin wata huld'a da k'ungiyar.

A bayanin da shugaban k'ungiyar, Cif Victor Okonkwo, ya yi wa manema labarai kwanan baya kan halin k'ak'a- ni-ka-yi da k'ungiyar ke ciki, ya ce sakamakon binciken da su ka yi, musamman kan Dokar Kafa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta 2001, k'ungiyar ba ta k'ark'ashin aikin hukumar.

Ya ce, “Mun karb'o kundin dokar daga Majalisar Dokoki ta Jihar Kano kuma ta nuna b'aro-b'aro cewa babban aikin hukumar shi ne kula da b'angaren finafinai da kuma gidajen silima, da kuma rubuce-rubucen tsiraici. Ban ga abin da ya had'a su da k'ok'arin ganin mun yi rajista da su ba. Mu mu na sana’ar sayar da littattafan manhaja ne na d'aliban makarantun firamare da sakandare. Mun yi amanna da cewa kamfanonin da ke wallafa su sun riga sun tace su.”

Ya ci gaba da cewa, “Bayan haka, mu na sha biyan haraji kala-kala ga K'aramar Hukumar Fagge da kuma Ma’aikatar Ciniki ta jiha. Zai kasance duka biyu idan kuma aka ce mu k'ara biyan wani sabon harajin ga Hukumar Tace Finafinai.

“Mu ba mawallafa ba ne, kuma ba mu huld'a da littattafan tsiraici. Mu na kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta shigo cikin wannan lamari don ta cece mu daga had'arin da mu ke ciki.”

Okonkwo ya k'alubalanci hukumar da ta kai k'arar k'ungiyar a kotu domin tabbatar da manufofin dokar da ta kafa ta, ya na mai k'arawa da cewa ko kad'an ba za su yarda a tatse ’yar ribar da su ke ci ba ta hanyar haraji maras kan-gado da hukumomin gwamnati ke son su biya.
Da aka tuntub'i shugaban hukumar don jin ta bakin sa, Malam Abubakar Rabo Abdulkarim ya yi watsi da k'orafe-k'orafen k'ungiyar, ya na mai cewa su hukuma su ne su ka fi kowa sanin tanade-tanaden dokar hukumar, ba wani mutum da yake daga waje ba wanda ke ganin wai shi ya san me dokar ta ce.

Ya ce da gaske ne dokar su ta shafi duk wani aiki na d'ab’i, ciki kuwa har da masu sayar da jaridu da littattafai, na nishad'i ne ko na makaranta. “Doka ta ba mu damar mu tabbatar da cewa wad'annan dillalan littattafan su na sana’ar su bisa abin da doka ta tanada, kuma tilas ne su zo su yi rajista mu ba su lasisi. A kan haka ne mu ke aiki,” inji shi.

Shugaban hukumar ya yi barazanar cewa kwanan nan hukumar za ta fara yak'i da wad'annan mutane, ya ce duk wanda hakan bai masa daidai ba to ya tafi kotu ya yi k'ara.


 

 

 

 

Daga ALIYU A. GORA II,
a Zariya

TUN ranar Litinin, 8 ga Yuni 2009, ’yan fim su ka samun sak'on gayyata daga Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Kwango, Zariya (Center For Islamic Legal Studies). Cibiyar sun gayyaci ’yan fim ne da sunan cewa Darakta Janar na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Abubakar Rabo Abdulkarim, zai zo ya yi lacca kan finafinan Hausa a ranar Lahadi, 21 ga Yuni. A takardar gayyatar, an nuna cewa za a ba duk d'an fim d'in da ke da abin cewa minti 10. Hakan ya sa ’yan fim, musamman manyan cikin su a Kaduna, su ka yi shirin yadda za su b'ullo wa Rabo a Zariya, mutumin da su ka dad'e su na neman yadda za su yi ido da ido da shi.

Da yake an ce kyakkyawar Juma’a tun daga Laraba ake ganewa, duk tattaunawar da ’yan fim d'in su ka yi a Zariya a k'ark'ashin jagorancin shugaban k'ungiya furodusoshi ta Jihar Kaduna, ko muk'addashin magatakardan k'ungiyar bai lek'a ba. ’Yan Zariyar kawai aka bari su ka yi kid'an su, su ka kuma taka rawar su. Duk da haka, kafin zuwan ranar da za a yi al’amarin, ’yan fim da dama sun yi ta d'okin zuwan ranar don su je su yi gwa da gwa da Rabo. Sai dai abin mamaki, har aka kammala babu wani d'an fim daga Kaduna da ya lek'a ko K'ofar Doka.
Taron, wanda aka yi shi a d'akin taro na jami'ar, an fara shi da misalin k'arfe 10:00 na safe kamar yadda aka tsara. Duk wani d'an fim da ya kwana ya tashi a Zariya ya samu halarta. Rabo kuma ya isa wurin da tawagar sa tun misalin k'arfe 9:30 na safe.

Bayan an gabatar da manyan bak'i, wad'anda ba sanannu ba ne, mafi yawancin su malaman makarantar ne, sai aka ba Rabo fili kai tsaye ya fara aiwatar da abin da ya kawo shi.

A jawabinn sa, Malam Rabo ya jadda cewa hukumar sa ba za ta bari ’yan fim su lalata kyawawan al’adu da addinin jama’ar Kano ba. Ya ce gwamnatin Kano ba za ta tab'a yin sassauci kan aikin ta na tsarkake jama’a ba da yin mulki bisa tanaje-tanajen addini.

Rabo ya ce, “Mu ba mu na yak'i da kowa ba ne, to amma tilas ne al’umma ta zauna ta san menene ya dace da ita kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ana cewa shi fim wani abu ne da ya had'o da rayuwar d'an’adam, da al’adun sa, addinin sa da kuma mu’amalar sa. Kamata ya yi ya yi mana jagora kan tunanin mu da kuma yadda za mu gina nagartacciyar al’umma. Aikin da ya rataya a wuyan mu ne, wanda ba za mu yi sassauci a kan aiwatar da shi ba.”

Ya ce ’yan fim su ne su ka lalata harkar fim, kuma su ka sa ana yi wa hukumar tace finafinai kallon hadarin kaji. Ya ce, “Ku na so duniya ta kalle mu a matsayin al’ummar karuwai da sauran ayyukan assha. Kuma ra’ayin mu shi ne fim ya na da kyau a wani b'angaren, sannan ya na da rashin kyau a wani b'angaren.”

Haka dai Malam Rabo ya yi ta ragargazar ’yan fim, ya ci kasuwar ya zauna.

Wani abin mamaki shi ne duk da cewa wad'anda su ka shirya laccar malamai ne, amma da lokacin salla ya yi, rok'on mutane aka yi cewa a hak'ura a ci gaba da sauraron jawabin Rabo domin, a cewar su, wai lokacin salla ba ya wucewa, kuma abin da su ke yi d'in shi ma aikin addini ne! Don haka ana ji ana gani azahar ta zo ta wuce, har la’asar ta shigo, ba a tashi aka yi salla ba.

Wani abin da ya rikitar da ’yan fim shi ne da farko dai ba a ce Rabo zai gabatar da k'asida ba, an ce dai zai zo ya yi “wa’azi a kan alfanu da illolin finafinan Hausa,” kuma za a ba da filin tambaya ga wanda ya ke da ita, wanda kuma ke da jawabi za a ba shi minti 10. Amma sai da Rabo ya kwashe kimanin awa biyu cur ya na jawabi bai dakata ba. Sannan daga k'arshe aka ce an ba ’yan fim biyu dama su yi magana ta minti uku-uku kowannen su. Tsohon shugaban K'ungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Malam Adamu Bello Ability, shi ne ya fara magana. Sai dai bayanin da ya gabatar ya kashe wa ’yan fim jiki. Da farko, kasancewar an san Ability d'an cara ne, ’yan fim sun yi tsammanin zai share masu hawaye ta fuskar k'alubalantar Rabo gadan-gadan. Maimakon haka, sai ya karkatar da akalar sa zuwa k'orafi a kan tsofaffin shugabannin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano da cewa su su ka lalata harkar fim kafin zuwan su Rabo. Wannan ya sa wasu ’yan fim d'in ke k'orafin kamar Ability ya na yabawa ne da yadda Rabo ya ke ci wa harkar fim tuwo a k'warya. Baya ga haka, Ability ya yi amfani da wannan dama ya shaida wa Rabo cewa gyaran da ya ke kiran a yi wa sana’ar fim, su a Zariya tuni sun yi nisa wajen shirye-shiryen d'auko masana da za su koyar da yaran su yadda ake gudanar da harkokin fim. A k'arshe, ya k'are jawabin sa da rok'on alfarma da cewa su na rok'on Rabo ya ba su gudunmuwa kan hakan.

Shi kuwa shugaban K'ungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Malam Hamisu Jibril Goma, k'alubalantar Rabo ya yi kai-tsaye a kan wani misali da ya bayar na cewa a Turai an yi wani fim da ya ke ganin kamar an ci zarafin Musulunci ne. Ya ce ya na ganin haka ya kamata a ce ’yan fim d'in Hausa su rik'a yi wajen d'aukaka addini da al’adun su. Shugaban ya k'alubalanci Rabo da cewa me ya sa hukumar sa ba ta shirya wani fim makamancin wancan d'in ba don mayar da martani? A k'arshen jawabin sa kuma ya jaddada wa Rabo cewa su a Jihar Kaduna su na da tsari na shugabanci da doka. Shi ya sa shi kan sa Rabo a jawabin sa ya keb'e

Kaduna da cewa ba ta daga cikin garuruwan da ake zargin ’yan fim sun gurb'ata, ko da ya ke dai ya ce garin Zariya ya na buk'atar garambawul.
Fahimtar da mafi yawacin jama’ar da su ka halarci taron su ka yi wa al’amarin ita ce da ma wad'anda su ka shirya laccar mutane ne da su ke k'yamar sana’ar fim da masu yin ta tun asali, ba ma su son a gyara kurakuran da ke ciki ba. Hakan ya tabbata ne a lokacin da wani malami mai suna Ahmed Bello Dogarawa, wanda ya ke d'aya daga cikin jiga-jigan malaman da su ka shirya taron, a jawabin sa na k'arshen taron ya ce ba ya son fim, ba ya son d'an fim, ba ya son ganin d'an fim, kuma babu abin da d'an fim zai yi ya birge shi a rayuwa.

“A gaskiya ba a yi wa ’yan fim adalci ba. In ba haka ba, ya za a tasa su a gaba ana ragargaza, amma aka hana su isasshen lokacin da su ma za su gabatar da nasu k'asidun?” inji wani d'alibi da ke zaune kusa da wakilin mu a wurin.

Akwai wani d'an fim da ya rik'a yunk'urin a ba shi dama ya yi magana. Amma nan take wani da ke kusa da shi ya ba shi shawara da cewa ya yi hak'uri. In kuwa ya kuskura ya fad'i abin da ya sab'a wa ra’ayin Rabo a wurin, zai sha kashin tsiya. Saboda akwai tunanin tarko ne aka d'ana wa ’yan fim d'in ko za a samu wanda zai yi maganar da ta sab'a wa mak'asudin taron. Da yawa sun yarda da wannan hasashen, musamman ganin yadda shugaban taron, Malam Ahmed Bello Dogarawa, ya tsare gida, wanda tun da aka fara har aka kammala babu wanda ya ga ko murmushin sa, don kada ma ’yan fim su yi tunanin samun sakin fuskar da zai iya sauraren su.

Bayan an fito daga d'akin taron, wakilin mu ya ji wani furodusa na cewa, “Wai ni me ya sa ma mu ka zo wannan wurin? Da na san an gayyato mu ne don a ci zarafin mu, wallahi da ban zo ba. Amma, gobe ma rana ce!”

An kammala taron lafiya da misalin k'arfe 3:00 na yamma. Manyan ’yan fim da su ka halarci taron sun had'a da Aminu Mirror, Musa Aminu (Carlos), Tukur Aliyu, da kuma Cashman. ’Yan wasa kuma da dama sun samu halarta, amma duk na cikin garin Zariya.

RAYUWAR IYALI
BABBAN LABARIN
 
 

WASIKU
Ku daina wulakanci
Ai ga irin ta nan!
Mu taya sani addu’a
Abin a yaba ne
Allah ya gafarta ma ta
Allah ya jikan jamila
Allah ya jikan binta
Sakon ta’aziyya da jaje
Ta’aziyya ga sheme
Ki canza rayuwar ki
Allah ya gafarta ma ta
Sako ga shehu kano
Mu ma mun sara mata
’Yan fim ga shawara
Dubi dai jamila haruna
jaje da ta’aziyya
Allah jikan rai
Aikin ku ya yi kyau
Matashiya ga ummancy
‘bolanle’ shirme ne
Ku hada ni da ali nuhu
Rashin ya shafi kowa
Allah ya ba sani lafiya
Sakon ta’aziyya
Fati nijar ta birge ni
Gaisuwa ga ma’aurata
Ku daina la’antar su
Ki na fa da aure!
Rabo mayaudari ne
Allah jikan su
Tahir da binta ina murna
A gaida nakwango
Fantimoti ga gyara
Na ga alfanun fim

LABARAI
An yi taron addu’a ga mamatan marubuta a Kano
’Yan fim na Katsina sun kai wa Rabo caffa
Kotu ta haramta wak'ok'in industiri guda 11
Jami’an Rabo sun fara farautar mawak'a
An Kama Ali Jita Saboda Wak'ar Biki
Mahaifiyar Safiya Musa Ta Kwanta Dama
Ummi Zee-Zee ta zama mawak'iyar Turanci
Zainab da Rabi’u Dalle sun samu Umar
K'ungiyar dillalai na so a raba ta da zalunci
An bugi ’yan fim an hana su kuka
 
     
   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
 

TOP

   
An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com