| Da
ya ke mafi yawanci finafinan da ta yi ba su riga
sun shiga kasuwa ba, 'yan kallo da dama za su
yi mata kallon bak'uwa. Sai dai a cikin industiri,
duk wanda ya kai ya kawo ya san da zaman ta.
Kai da ganin ta ka san ta dace a ce ita ce jarumar
fim d'in ka. Ga ta dai da kyau, ga kyan launin
fata, ga kyan diri, ga fara’a, ga tsafta,
ga natsuwa da biyayya musamman ga na gaba da ita.
Sannan jarumar ta samu shaidar zama d'aya daga
cikin jaruman da ba su cika tsegumi ba a lokacin
da ake aikin fim a lokeshin.
Sai dai abin tambaya game da Safiya shi ne, me
ya sa ita yanzu ta ga wurin zama a industiri,
yayin da wasu ke rantawa a na kare su na canza
alk'ibla? Me ta ke ciki? Menene burin ta dangane
da harkar fim? Ya zancen auren ta? Menene matsayin
ta ga gwamnatin Jihar Kano? Shin ita ma ta na
da ubangida kamar yadda sauran taurari mata su
ke yi? Jarumar duk ta amsa wad'annan tambayoyin
da ma wasu a tattaunawar musamman da ta yi da
wakilin mu kwanan baya a birnin Kano.
FIM: Safiya, kwana biyu. Yaya industiri?
SAFIYA: To, ga mu nan a ciki ana gogawa.
Me za ki iya cewa game da halin da industiri
ta shiga?
Babu abin da za mu ce sai dai mu ce Allah Ya
sa haka shi ne mafi alkhairi. Allah Ya gyara mana
wannan sana’a tamu. Kuma duk abin da ka
ke yi a rayuwa da ma in har ba a jarrabe ka ba
a kan abin da ka ke yi, to ya kamata kai ma ka
tambayi kan ka.
Har yanzu kenan ki na cikin harkar ba ki bar
ta ba, kamar yadda wasu su ka yi. Ke me ya sa
har yanzu ana gogawa da ke?
Alhamdu lillahi. Gaskiya ni dai babu abin da
zan ce, domin kusan d'aukaka ce ta zo bayan komai
ya d'an lafa. Finafinan da aka rik'a yi a wajen
Kano kusan duk da mu aka rik'a yi. Ak'alla yanzu
ina da finafinai manya da ni ce na ke jan su.
Misali kamar fim d'in ‘Fargaba’, ‘Mai
Doki’, ‘Biyayya’, da dai sauran
su.
Yanzu a k'ark'ashin wane kamfani ki ke?
Ina nan a kamfanin ubangida na Jamilu mai kamfanin
Almubarak.
Amma da muka ji an ce kin koma kamfanin 2-Effects...
A’a, ina nan a kamfanin ubangida na. Su
ma 2-Effects kamar kamfani na ne, domin suna taimaka
min. Su na yi min finafinai, don ko 'Mai Doki'
ma fim d'in kamfanin su ne.
Menene yanzu ki ke ganin ya sa ana ta gayyatar
ki yin finafinai?
Ka san komai daga Allah ne. Ina ganin lokaci
ne, domin komai ka gani daga Allah ne. D'aukaka
ce na samu daga Allah.
Duk finafinan da ki ka yi yanzu a ina aka yi
su?
An yi wasu a Kaduna, wasu kuma a Abuja.
A cikin finafinan da ki ka yi yanzu wanne ne
ki ka fi so, ko ki ka fi shan wahala, ko kuma
wanda ba ki tab'a yin irin sa ba?
Fim d'in ‘Fargaba’ shi ne fim d'in
da ban tab'a yin irin sa ba. Kuma fim d'in ya
burge ni sosai. Sannan kuma fim d'in ‘Biyayya’,
shi ne fim d'in da na sha wahala a cikin sa. Sannan
irin yadda a fim d'in 'Fargaba', ko yaushe ina
cikin fargaba, ya sa kusan ji na ke kamar ma da
gaske ake yin komai. Kuma irin rol d'in da Baballe
da A'isha Abaab su ka hau ya burge ni. Sannan
kuma fim d'in ya ci sunan sa, domin kusan kowa
a fim d'in a cikin fargaba ya ke, kai ka ce da
gaske ake yin komai a fim d'in.
Kin ambaci wani fim mai suna 'Biyayya', shi kuma
na wanene?
Fim d'in Hafsat Sulaiman ne. Wannan fim d'in
na sha wahala a cikin sa ba kad'an ba.
A kan me fim d'in ya ke nuni har ki ka ce kin
sha wahala sosai a cikin sa?
Fim d'in ya na koyarwa ne kan irin yadda iyayen
miji su ke takura wa matar d'an su, da d'ora mata
abin da ba ita ta yi ba.
An ce ki na da alak'a da ita Hafsat. Mecece dangantakar
ku da ita?
Baba ce a wuri na. Yayar ta ta na auren wan baba
ta.
Ga shi yanzu kin halarci bikin Binta da Tahir,
ke kuma yaushe za a yi naki?
Lokaci na ke jira. Domin da mutuwa da aure duk
lokaci ne na Ubangiji. Ina nan ina rok'on Allah
Ya kawo min mai so na. Su kuma da Allah Ya k'addara
nasu auren yanzu, ina yi masu fatan alkhairi da
zaman lafiya da kuma zuri’a d'ayyiba.
Ki na nufin ki ce har yanzu ba ki da saurayi,
ko da a industiri?
Ba ni da saurayi a industiri. Amma ina da ubangida.
Ni sana'ar fim ta kawo ni ba wannan ba.
Ki na ganin za ki iya yin aure a daidai wannan
lokacin da za a iya cewa ke ma tauraruwar ki ta
na haskawa?
Me zai hana ni yin aure? Ai in ka ga ban yi ba
ko ba a yi ba, to lokacin ne bai yi ba. Amma muddin
lokacin ya yi, za ka ga sai dai labarin Safiya
a industiri.
Kusan duk jaruman industiri sun yi rajista da
gwamnatin Jihar Kano. Ke ma kin yi ko yaya?
Na’am, na yi rajista ni ma.
Menene dalilin ki na yin rajista da gwamnati?
Kawai na fuskanci cewa gwamnati ta na son yin
gyara ne a wannan harkar tamu. Kuma duk wani abu
da ya faru a baya game da wannnan harkar, kawai
mu ajiye shi a gefe, mu tsaya mu had'a kan mu.
In dai mu ka yi wannan, to duk wani mai neman
nak'asun mu zai yi ma ya bari.
Ki na ganin shigowar gwamnati a harkar fim da
alamun wasu abubuwan na ci gaba ne?
Gaskiya duk wani abu, kamar yadda na ce, in ka
na yi har ba ka samu matsala a ciki ba to ka tambayi
kan ka. Akwai alamun ci-gaba shigowar gwamnati
cikin harkar nan.
Menene kiran ki ko shawara ga abokan sana’ar
ki?
Kira na ba ya wuce in ce mu ci gaba da yin addu’a.
Kuma ina kira da mu ji tsoron Allah, mu so junan
mu. |