BABBAN LABARIN

RABO DA MARUBUTA SUN MAIDA WUK'AR

Sakamakon zuwan da shugabannin k'ungiyar ANA ta k'asa su ka kawo birnin Kano, akwai alamun samun sa’ida tsakanin marubutan Kano da Hukumar Tace Finafinai da D'ab’i ta Jihar Kano a kan rikicin tace littattafai da marubuta

Daga SANI MAIKATANGA da IBRAHIM MUSA GIGINYU, a Kano

DA alama, takun saar da ya fara faruwa tsakanin marubutan littattafai da Hukumar Tace Finafinai da D'ab’i ta Jihar Kano zai ragu idan har aka aiwatar da yarjejeniyar da aka cimmawa a ranar 25 ga Agusta, 2008. A ranar, shugaban {ungiyar Marubuta ta Nijeriya (Association of Nigerian Authors, ANA), Dakta Wale Okediran, ya kai ziyara a Hukumar Tace Finafinai da D'ab’i ta Jihar Kano don ganawa da shugaban hukumar, Malam Abubakar Rabo Abdulkarim. Ziyarar ta biyo bayan sa-katsi-sa-tokan da ake yi ne tsakanin marubutan, wad'anda hukumar ta ce za ta fara yi wa rajista, su kuma su ka ce ba su yarda ba. An yi cacar baki tsakanin jami'an hukumar da marubutan a wurare da dama. Ziyarar su Okediran ta faru ne don neman sasanta b'angarorin biyu.

Tun kafin a shiga d'akin ganawar, sai da aka aiwatar da wani taro tsakanin hukumar tace fiafinai da kuma jami'an k'ungiyar ta ANA.

Da fako dai shugaban na ANA ya fara ne da mik'a godiyar sa ga Malam Rabo bisa amincewar da ya yi kan gudanar da wannan ganawar. Ya kuma buk'ace shi da ya mik'a masa sakon fatan alheri ga Gwamnan jihar saboda irin goyon bayan da ya ke ba wa marubuta a jihar. Ya ci gaba da cewa ba zai tab'a mancewa da Kano ba, domin a taron marubuta na k'asa baki d'aya da aka yi a Kano a cikin 2005, shi ne ya samar da wannan shugabanci nasa da na sauran shugabannin kwamitin zartaswa na ANA.

Ya ce, “Kano jiha ce mai cike da d'imbin tarihi na rubuce-rubuce. Saboda haka 'ya'yan ANA da ke wannan jihar ke da matuk'ar k'ima a idon marubuta na gida da ma na waje. Dalilin kenan da ya sa mu ke ganin duk wani abu da ya samu ANA ta Kano to wannan abin ya shafi ilahirin duk wani marubuci da ke wannan k'asar.”

Okediran ya ci gaba da yin bayani kamar haka: “Na tsaya gaban wannan taron bisa doron tsari irin na ci-gaban d'an’adam don gabatar da ra'ayin k'ungiyar mu a kan batun rubutu da kuma maganar tacewa wanda wannan ya kasance matsalar da ta k'i ci ta k'i cinyewa a wannan jiha mai girma, wato Jihar Kano.

“Tun lokacin da kafafen yad'a labarai su ka fara d'aukar wannan labari, mu a matakin shugabanci a wannan k'ungiya mun fahimci cewar akwai matsala ta fahimta. Domin mu mu na gani matsalar ba matsala ba ce wacce za a kasa shawo kan ta ta hanyar zama bisa teburin shawara da kuma tattaunawa don fahimtar juna. Hakan shi ya sa mu ka yi maza-maza mu ka amsa kukan ’ya’yan wannan k'ungiya da ke Kano. Ba za mu nad'e hannuwan mu ba ga duk wani abu da zai kawo mishkila ga damar da marubuci ke da ita wajen yin rubutu da bugawa. Kuma wannan ba ya na nufin mu na adawa da tattaunawa da Hukamar Tace Finafinai da D'ab’i ba ne don samun maslaha; hasali ma ina mai farin ciki da wannan damar ta samu a yau d'in nan, 25 ga watan Agusta, 2008.”

Da ga nan shugaban ya yi bayani mai tsayi kan yadda aka samar da k'ungiyar ANA shekaru 26 da su ka wuce, k'ungiyar da a yanzu ta ke da rassa a jihohi 36 da ke wannan k'asar. Shugaban ya yi bayani kan yadda k'ungiyar ke ba da gudunmuwa wajen gina k'asa ta b'angaren ilmi, ci-gaban al’adu, zaman lafiya, da dai sauran su.

Okediran ya yi tsokaci game da yadda marubuta su ke kasancewa, inda ya ce, “Muhalli, ilmi, k'warewa da sauran su na da matuk'ar tasiri a kan marubuci. Wannan na nufin ’ya’yan ANA na Kano na sane da nauyin da ke kan su na kare addinin su, al’adar su, wajen samar da ingantattun littattafai. Duk da cewar mazauna Kano ne amma sun san rubuce-rubucen su ba na iya Kano kad'ai ba ne, har da duniya baki d'ayan ta. Haka zalika k'ungiyar ANA ba za ta amince da duk wani nau’in rubutu wanda zai iya gurb'ata tarbiyya ko al’ada ba. Ga mu ’yan k'ungiyar ANA, buk'atar marubuci ya kawo littafin sa a tantance kafin a ba shi dama ya buga, nak'asu ne ga fasahar sa, domin tarihi ya nuna ba a tab'a yin haka ba. Kuma yin hakan ba zai haifar wa Jihar Kano wata martaba ba gida da waje.”

A k'arshe, shugaban ya mik'a goron gayyata ga hukumar zuwa wajen taron marubuta na duniya, wato Annual International Convention karo na 27 da za a gudanar a ranar 31 ga Oktoba, 2008 a Gusau, Jihar Zamfara.
A nasa jawabin, Malam Rabo ya nuna farin cikin sa da samun damar karb'ar bak'uncin shugaban na ANA. Ya kuma nuna jin dad'in sa bisa wannan zama da za a yi na tattaunawa, wanda shugaban ya ce sun dad'e suna neman a yi hakan amma abin ya ci tura. Haka zalika ya nuna rashin jin dad'in sa ga yadda kafafen yad'a labarai su ka yi ta fuskantar al’amarin ta bari d'aya kawai, inda ya ce, “Abin b'acin rai ne yadda na ga mutane akilai na yin rubuce-rubuce marasa manufa wad'anda su ka karkata b'angare d'aya kawai. Duk da wannan bai sa mun d'au al’amuran da zafi ba, sai mu ka yi amfani da hankali, kasancewar amfani da hankali na d'aya daga cikin abin da aka raine mu bi san sa.”

Shugaban ya ci gaba da cewa ya ji dad'in yadda a bayanin sa, Okediran ya fahimci cewar akwai matsala ta fahimta. Ya k'ara da cewa bayan wannan akwai matsala ta yad'a ji-ta-ji-ta da gangan don alak'anta wannan maganar ta marubuta da wata magana da ba ta marubuta ba. Domin, inji shi, akwai ’ya’yan ANA masu gida biyu, wato marubuta ne kuma watak'ila masu harkar fim ne, ko masu gudanar da gidajen sinima, da dai makamankan hakan. Kasancewar harkar fim, sinima da sauran ire-iren wannan harkar duk su na k'ark'ashin kulawar wannan hukumar ne.

Rabo ya yi murna da kuma karb'ar goron gayyatar da k'ungiyar ANA ta mik'a masa na taron da za ta yi a Gusau. A k'arshe ya ce, “Doka ita ta kafa mu, kuma ba za mu kasance masu wofinta doka ba. Saboda haka duk wani abu da za mu yi, za mu yi shi ne bisa farfajiyar da doka ta tanadar.”

Daga nan sai aka kori ’yan jarida. Sannan b'agarorin biyu su ka shiga tattaunawa ta sirri, wanda wannan tattaunawar ta kai ga samar da takardar bayan taro wacce kuma aka rarraba wa ’yan jaridu ita.
A tsarin wannan ziyarar shugaban na ANA ta k'asa zai gana da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano a Gidan Gwamnati na Kano a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2008.

Haka kuwa aka yi. Washegari, shugaban na ANA ya kai ziyara Gidan Gwannatin inda mai girma Mataimakin Gwamna, Injiniya Abdullahi Muhammed Gwarzo, ya karb'e shi tare da ’yan rakiyar sa, wad'anda su ka had'a da shugabannin rassan k'ungiyar daga jihohin Kano, Katsina, Zamfara da Sakkwato. A bayanin sa, Dakta Okediran ya sanar da mataimakin gwamnan cewa shugabancin ANA na k'asa da kuma Hukumar Tace Finafinai da D'ab’i ta Jihar Kano sun zauna a jiya don samun fahimta da kuma damar gudanar da ayyukan su kan tafarkin taimakekeniya.

Ya k'ara da cewa cikin matsayar da aka cimma har da amincewar da hukumar ta yi na a gudanar da taron k'ara wa juna sani wanda za ta gudanar nan ba d'a dad'ewa ba. Ya kuma nuna farin cikin sa bisa karb'ar goron gayyatar zuwa babban taron ANA na k'asa da za a gudanar a Gusau da hukumar ta yi. Ya ce, ‘‘Ina mai amfani da wannan damar wajen yaba wa mai girma Gwamnan Jihar Kano saboda irin gudunmawar da ya ke ba harkar ilmi a Jihar Kano. Haka kuma mun lura da cewa d'akin karatun da ke ofishin mataimakin gwamna na fama da matsakar rashin littattafai. Sabod haka mu ke masu amfani da wannan dama wajen ba da gudunmuwar littattafai ga wannan d'akin karatu. A matsayin wani b'angare na fatan alkhairi ga gwamnati. Mu na masu godiya da wannan dama da aka ba mu, kuma mu na masu addu’ar Allah Ya ci gaba da yi wa wannan gwamnati jagora.”

A nasa jawabin, Injiniya Abdullahi Muhammad Gwarzo ya mik'a sak'on maraba ga shugaban na ANA na k'asa a madadin gwamnan jihar da mutanen jihar. Ya kuma k'ara ba da hak'uri bisa jinkirin da aka samu wajen ganawar tasu. Ya ci gaba da cewa, “Gwamnati wannan jiha gwamnati ce mai bai wa kowa ’yancin sa yadda tsarin mulkin k'asa ya shimfid'a. Haka zalika aikin mu ne mu d'ora jama’a bisa wannan turbar, dalihin da ya sa aka kafa wannan hukumar ta tace finafinai da d'ab’i.”

Mataimakin gwamnan ya yi wata magana wadda ta dad'ad'a wa k'ungiya ANA rai sosai har sai da ta kai da an tafa masa. Maganar kuwa ita ce: ‘‘Hak'k'in wannan hukumar ne sa ido a harkar rubuce-rubuce, talifi da kasuwancin littattafan. Na yi matuk'ar namaki da wai marubuta kan su an sako su cikin wannan tsarin. Na san kun sami zama a jiya, kun kuma cimma matsaya. Mu kuma a nan a shirye mu ke da mu yi aiki da duk wata yarjejeniya da wannan zama naku ya samar. Kuma ina mai fatan wannan matsaya da aka cimma zai amfana mana mu da mutanen Kano baki d'aya.’’

Injiniya Gwarzo ya kuma yi wa ’ya’yan ANA ta Kano albishirin cewa gwamnatin jihar za ta d'au nauyin su wajen halartar taron k'ara wa juna sanin da za a yi. Ya kuma yi kira ga ’ya’yan k'ungiyar ta ANA da su isar da wannan sak'on na gwamnati ga duk wani memba nata. Ya kuma yi kira da cewar babu wata hujja ta sa-in-sa tsakanin gwamnati da k'ungiyar marubutan, domin dukkan su abokan aiki da juna ne. A k'arshe ya yi wa shugaban ANA ta k'asa fatan alkhairi da kuma addu’ar Allah Ya mai da shi gida lafiya.

Haka dai aka fito daga taron ana ta murmushi da jinjina wa juna. Kowa ya na da yak'inin cewa wannan zama da aka yi da Malam Rabo da kuma mataimakin gwamna ya kawo k'arshen sa-in-sar da ta shiga tsakanin marubutan da gwamnati. To amma wani jami’i na k'ungiyar ANA ta Kano ya yi gargad'in cewa kada marubuta su yi sakacin yin barci da dukkan idanun su a rufe. Ya ce ya kamata a ci gaba da sa ido kan abubuwan da hukumar Rabo ta alk'awarta, “domin ba mamaki Rabo ya k'ara zuwa gidan rediyo ya b'ata marubuta - saboda haka ya dinga yi wa 'yan fim bayan sun yi zaman sasantawa.”

RAYUWAR IYALI
BABBAN LABARIN
 
 

WASIKU
Ku daina wulakanci
Ai ga irin ta nan!
Mu taya sani addu’a
Abin a yaba ne
Allah ya gafarta ma ta
Allah ya jikan jamila
Allah ya jikan binta
Sakon ta’aziyya da jaje
Ta’aziyya ga sheme
Ki canza rayuwar ki
Allah ya gafarta ma ta
Sako ga shehu kano
Mu ma mun sara mata
’Yan fim ga shawara
Dubi dai jamila haruna
jaje da ta’aziyya
Allah jikan rai
Aikin ku ya yi kyau
Matashiya ga ummancy
‘bolanle’ shirme ne
Ku hada ni da ali nuhu
Rashin ya shafi kowa
Allah ya ba sani lafiya
Sakon ta’aziyya
Fati nijar ta birge ni
Gaisuwa ga ma’aurata
Ku daina la’antar su
Ki na fa da aure!
Rabo mayaudari ne
Allah jikan su
Tahir da binta ina murna
A gaida nakwango
Fantimoti ga gyara
Na ga alfanun fim

LABARAI
An yi taron addu’a ga mamatan marubuta a Kano
’Yan fim na Katsina sun kai wa Rabo caffa
Kotu ta haramta wak'ok'in industiri guda 11
Jami’an Rabo sun fara farautar mawak'a
An Kama Ali Jita Saboda Wak'ar Biki
Mahaifiyar Safiya Musa Ta Kwanta Dama
Ummi Zee-Zee ta zama mawak'iyar Turanci
Zainab da Rabi’u Dalle sun samu Umar
K'ungiyar dillalai na so a raba ta da zalunci
An bugi ’yan fim an hana su kuka
 
   
 
An fara buga mujallar Fim (ISSN 1595-7780) a cikin Maris 1999. Ta na fitowa a kowane wata daga kamfanin INFORMART PUBLISHERS LTD., No. AK 6, Yoruba Road, Kaduna, Nijeriya. Ofishin mu a Kano: Ofishin mujallar Concern, 2nd Floor, Hadiza House, daura da Masallacin Umar Ibn Khattab, Zaria Road, Kano.
A aiko da dukkan wasiku ta adireshin mu na I-mel: mujallarfim@yahoo.com